“Zan Iya Zama Ta 3 Ko 4”: Budurwa Ta Yi Nutso a Son Bello El-Rufai, Tana So Ya Aureta

“Zan Iya Zama Ta 3 Ko 4”: Budurwa Ta Yi Nutso a Son Bello El-Rufai, Tana So Ya Aureta

  • Wata matashiyar budurwa ta garzaya dandalin soshiyal midiya don sanar da duniya irin son da take yi wa Bello El-Rufai
  • Bello shine 'dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa, kuma 'da ne a wajen tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai
  • Matashiyar ta bayyana a shafinta na X cewa a shirye take ta shiga gidan 'dan majalisar a matsayin mata ta uku ko hudu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matashiyar budurwa ta haddasa cece-kuce a dandalin soshiyal midiya bayan ta ayyana soyayyarta ga 'dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai.

Bello ya kuma kasance 'da ne a wajen tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai.

Matashiya ta zautu kan son Bello El-Rufai
“Zan Iya Zama Ta 3 Ko 4”: Budurwa Ta Yi Nutso a Son Bello El-Rufai, Tana So Ya Aureta Hoto: @Afeeyahtuh
Asali: Twitter

Matashiyar mai suna @Afeeyahtuh a dandalin X ta cire kunya a matsayinta na 'ya mace, don tabbatar da irin son da take yi masa.

Kara karanta wannan

Rayuka 7 sun salwanta saboda turmutsitsi a wajen siyan shinkafar kwastam a jihar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Afrah ta kuma sha alwashin zama ta uku idan mata biyu ne da shi, koma ta hudu idan ya zamana sun kai uku.

Sai dai kuma, ta roki 'dan majalisar da ya saki daya daga cikin matan nasa idan har sun kai hudu domin ta samu damar shiga cikin jerin matan nasa.

Kamar dai yadda yake bisa koyarwar addinin Musulunci, namiji na da damar aure mata biyu, uku zuwa hudu ne kawai.

Ta rubuta a shafin nata:

"Wallahi ina son Bello Elrufa’i kuma ina son auren ka!!
"Idan matar ka daya zan zama ta biyu, idan matan ka biyu zan zama ta uku, idan matan ka hudu Don Allah ka saki daya ka aure ni ."

Jama'a sun yi martani kan bukatar budurwar

Masu amfani da shafin X sun bayyana ra'ayoyinsu kan bukatar budurwar, inda wasu suka yi zargin cewa kudinsa budurwar ke so.

Kara karanta wannan

"Ban san me ya hau kaina ba": Matashi ya sheke mahaifiyarsa, ya kona gidansu

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@KawuGarba ya yi martani:

"Allah bazai barki ki yaudari Audu ba.
"Kiyi hakuri kawai da wanda Allah ya baki a layinku."

@JagoraArc ya yi martani:

"Kudin shi kike so wallahi Kina tallar kanki karshen duniya kenan ko kunya bakia ji wallahi Babu Daraja."

@BUSADEEQ ya ce:

"Sbd yana d kudi ba soyayya sbd Allah ynx."

@officialfateema ta ce:

"Kiyi fatan Allah ya baki nagari amma wnn kofa a rufe take."

@Abdallahsalees2 ya yi martani:

"Kuma da gaske kike ??"

@Nazeeer_ ya ce:

"Son kwadayi ne, kuma ko kin sami miji ta hanyar nuna kwadayin kudinsa bazai taba darajaki ba."

@DonSuraj17 ya ce:

"Lalle kin dauko dala ba gammo..."

Uba ya kai diyarsa dakin miji da kansa

A wani labarin kuma, mun ji cewa kamar yadda aka saba bisa al'adar Mallam Bahaushe da mutanen Arewa, a duk lokacin da aka ce za a kai amarya dakin mijinta, 'yan uwa da abokan arziki kan taru su yi mata rakiya.

Sai dai kuma, wani uba da aka yi auren diyarsa a kwanan nan, ya yi watsi da wannan al'ada, inda ya zabi aiki da koyarwar addini a madadin haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng