EFCC Ta Saki Adadin Miliyoyin da Aka Karbo a Hannun Barayi Daga Zuwan Olukoyede

EFCC Ta Saki Adadin Miliyoyin da Aka Karbo a Hannun Barayi Daga Zuwan Olukoyede

  • Za a iya cewa Ola Olukoyede ya tabuka abin da ya cancanci yabo daga lokacin da ya karbi jagorancin hukumar EFCC zuwa yanzu
  • Shugaban na EFCC ya ce an karbo N60bn da wasu makudan miliyoyin kasar waje bayan zamansa shugaban hukumar a shekarar 2023
  • Ola Olukoyede ya bada labarin yadda a karshen bara EFCC ta hana a sulale da wasu kudi da ake zargin na sata ne ta asusun banki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban hukumar EFCC na kasa, Ola Olukoyede, ya shaida yunkurin da suke yi na cafke masu aikata rashin gaskiya.

Punch ta ce Ola Olukoyede ya ce hukumar da yake jagoranta tana so ta ga bayan wadanda ake zargi da barna a Najeriya.

Kara karanta wannan

25kg kan N10k: Kwastam ta fara siyar da shinkafa a farashi mai rahusa, ta fadi inda za a samu

EFCC.
Sabon shugaban EFCC Ola Olukoyede a Aso Villa Hoto: @OfficialEFCC/www.reuters.com
Asali: UGC

EFCC za ta binciki laifuffuka 3, 000

Shugaban na EFCC yake cewa akwai korafi da koke-koke sama da 5, 000 da aka kai gabansu, daga ciki ne za a binciki 3, 000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olukoyede ya yi jawabin ne da aka gayyace shi domin gabatar da lacca a wata cibiya a Legas da tayi bikin shekaru 20 da kafuwa.

A wajen ne shugaban hukumar yaki da rashin gaskiyan ya ce a cikin watanni hudu rak da rantsar shi, an kabo makudan kudi.

Nawa EFCC ta karbe a mulkin Tinubu?

EFCC da aka kafa a shekarar 2000 ta karbo N60bn da $10m daga hannun bata-gari.

Baya ga haka, a karkashin jagorancin Olukoyede, hukumar ta EFCC ta samu nasara kusan 700 a shari’ar da aka yi da ita a gaban kotu.

A daren 31 ga watan Disamban 2023, sabon shugaban EFCC ya ce ya toshe yunkurin tura wasu N40bn da ake zargin kudin sata ne.

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar EFCC sun cafke ɗaliban jami'ar Arewa, sun aikata wani babban laifi

Barayi sun damu hukumar EFCC

Olukoyede ya koka a game da yadda rashin gaskiya ya zama ruwan dare a ma'aikatu. New Telegraph ta fitar da rahoton nan ranar Lahadi.

EFCC ta ce yanzu an fito da dabarun zamani domin rage ko ma a kawo karshen satar dukiyar gwamnati da aikata miyagun laifuffuka.

Kafin a yaki barnar gaba daya a Najeriya, shugaban na EFCC ya ce dole kowa ya tashi tsaye, a hada-kai da kungiyoyi da ‘yan jarida.

Bola Tinubu da cire tallafin man fetur

A wani rahoto da muka fitar, ana ji Babachir David Lawal ya ce bai dace a soke tsarin tallafin fetur ba tare da tare tuntubar kowa ba.

Kafin Olusegun Obasanjo ya cire tallafi sai da ya kirkiro SURE-P, yake cewa Sani Abacha ya kafa PTF da ya tashi kara kudin fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng