Tsadar Siminti: Yadda Wasu Maza 2 Suka Dukufa Ginin Gida Babu Siminti, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Tsadar Siminti: Yadda Wasu Maza 2 Suka Dukufa Ginin Gida Babu Siminti, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Bidiyon wasu matasa biyu da ke aikin gina gida bayan sun kwaba jar kasa ya bayyana a soshiyal midiya kuma mutane sun tofa albarkacin bakunansu
  • Wani mutumi da ya yada bidiyon, ya bayyana cewa gini babu siminti shine mafita a yanzu, yana mai cewa kakanninsa sun gina gidajensu ta haka ne
  • Jama'a sun yi martani kan bidiyon inda mutane da dama suka caccaki hanyar da matasan suka bi wajen gida gidan

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga wani bidiyo na wasu matasa biyu da ke gina gida ba tare da amfani da siminti ba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar siminti a fadin kasar wanda ya jefa 'yan Najeriya cikin wani yanayi.

Kara karanta wannan

Ana karbar kebura: Bidiyon wani matashi da ke shan garin kwaki da man ja ya girgiza intanet

Wasu matasa sun kama gini babu siminti
Tsadar Siminti: Yadda Wasu Maza 2 Suka Dukufa Ginin Gida Babu Siminti, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce Hoto: @ojmoney55
Asali: TikTok

@ojmoney55 wanda ya yada bidiyon a dandalin TikTok ya nuna karfin gwiwa game da yadda irin wannan gini ke karko, yana mai cewa kakakkinsa sun gina hadaddun gida da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kakanninsa sun yi rayuwar farin ciki a gidajen da aka gina ba tare da siminti ba kuma sun auri mata fiye da daya.

Jaridar Legit ta rahoto cewa masu sarrafa siminti sun bayar da sharadin karya farashin siminti.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan ginin gida babu siminti

blessed lizzy collection ta ce:

"Hanya mafi kyawu."

Tella ta ce:

"Bandaki kake ginawa don dai kicin a zamanin nan ya fi wannan ginin da kake girma."

ObumRicher ya ce:

"Abun takaicina shine cewa ba za ka sake nuna shi ba idan ya ruguzo."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai kazamin hari kan matafiya, sun tafka mummunar ɓarna a jihar Arewa

Sam Sammy Suke ya ce:

"Yadda kuke kammala ginin wannan gidan ku tuna ku siya hular kwano faaaaa."

Goddy A. ya ce:

"A cikin nan aka haife ni kuma na girma na zama hadadden gaye."

Kamfanin BUA zai gwangwaje ma'aikata

A wani labari na daban, mun ji cewa a wani muhimmin mataki na ba da fifiko kan jin daɗin ma'aikata, Abdul Samad Rabi'u, shugaban rukunin kamfanonin BUA, ya amince da ƙarin kaso 50% na albashi ga ma'aikatansa.

An bayyana matakin ne ta hanyar wata sanarwa ta cikin gida daga shugaban ma’aikata na rukunin BUA, Mohammed Wali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel