Za a Dauke Wutar Lantarki a Ranakun Asabar da Lahadi a Birnin Tarayya Abuja, TCN
- Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa wasu sassa a Abuja za su shafe awanni bakwai ba tare da wuta ba
- A cewar wata sanarwa daga TCN, za ta gudanar da aiki kan wasu manyan na'urorin rarraba wutar lantarki a ranakun Asabar da Lahadi
- TCN ta ce yankunan Garki, Asokoro, Lugbe, Gudu, Gaduwa da sauran su ne abin zai shafa, tare da fatan za su yi hakuri kan katsewar wutar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Za a dauke wutar lantarki a wasu sassa na Abuja, babban birnin Najeriya na sa'o'i bakwai a ranakun Asabar da Lahadi, in ji kamfanin rarraba wutar na Najeriya (TCN).
TCN ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban manajan hukumar, sashen hulda da jama'a, Ndidi Mbah ya fitar a ranar Asabar rahoton Daily Trust.
Mbah, ya ce za a yi wasu 'yan gyare-gyare ne a kan manyan na'urorin rarraba wutar lantarkin masu karfin 132/33kV 2X100MVA a cikin tashar rarraba wutar ta Apo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mbah ya lissafa wuraren da za su fuskanci katsewar wutar lantarki kamar Garki, Asokoro, Lugbe, Titin Airport, Gudu, Gaduwa, sassan Lokogoma, Apo, Kabusa, Guzape da Nepa Junction.
Abin da sanarwar TCN ta kunsa
The Punch ta ruwaito cewa TCN za ta gudanar da aikin ne daga karfe 9:00 na safe zuwa 4:00 na yamma a ranakun Asabar da Lahadi.
“Saboda haka, za a samu katsewar wutar lantarki a kowacce 'taransfoma', kuma Abuja DisCo ba za ta iya raba wutar ga abokan huldarta ba.
Sanarwar ta kara da cewa:
"TCN ta yi nadamar rashin jin dadi da wannan aikin zai iya haifar wa ga masu amfani da wutar a yankunan da abin ya shafa."
Majalisar Dattawa ta nuna adawa da janye tallafin lantarki
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta ce ba ta amince da kudirin Shugaba Tinubu na janye tallafin wutar lantarki ba.
Sanatan Adamawa ta Tsakiya, Aminu Iya Abbas ne ya fara gabatar da kudirin adawa da matakin shugaban kasa yana mai cewa lokacin janye tallafin bai kamata ya zama yanzu ba.
Dan majalisar ya bijiro da batun janye tallafin wutar lantarki a wannan hali da kasar ke fama da matsin tattalin arziki ba abu ne da zai haifar da ɗa mai ido ba.
Asali: Legit.ng