25kg Kan N10k: Kwastam Ta Fara Siyar da Shinkafa a Farashi Mai Rahusa, Ta Fadi Inda Za a Samu

25kg Kan N10k: Kwastam Ta Fara Siyar da Shinkafa a Farashi Mai Rahusa, Ta Fadi Inda Za a Samu

  • Hukumar kwastam ta ce za ta fara siyar da kayan abinci kan farashi mai sauki a hekwatar hukumar ta 'Zone A' da ke Yaba
  • Kwanturola Janar Adewale Adeniyi ya sanar da cewar za a siyarwa talakawan Najeriya da buhun 25kg kan N10,000
  • Sauran kayan abincin da za a siyar sun hada da wake, masara, gero, waken suya, buhu 963 na busasshen kifi da sauransu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Hukumar kwastam ta sanar da cewar za a fara siyarwa jama'a da shinkafa da sauran kayan abinci a Legas da sauran yankunan kasar daga yau Juma'a, 23 ga watan Fabrairun 2024.

Za a siyar da kayan abincin ne a hedkwatar hukumar na 'Zone A' kan hanyar Harvey a Yaba.

Kara karanta wannan

Kwastam ta fara raba wa talakawan Najeriya kayan abinci da ta kwace, ta fadi ka'idojin cin gajiyar

Hukumar ta fara siyarwa talakawan Najeriya da kayan abinci
25kg Kan N10k: Kwastam Ta Fara Siyar da Shinkafa da Kayan Abinci a Rahusa Ta Fadi Inda Za a Samu Hoto: Nigerian Custom, Alamy
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto cewa babban kwanturola Adewale Adeniyi, ya ce za a siyarwa talakawan Najeriya da buhun 25kg kan N10,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeniyi ya yi ikirarin cewa umurnin shugaba Tinubu yana daga cikin alkawarin da ya dauka na karfafa tsaron abinci.

Ya ce:

“Halin da ake ciki na yawan fitar da muhimman kayan abinci daga kasar nan yana da ban tsoro kuma yana kawo babbar barazana ga tsaron abinci.
"Mun samu amincewa daga gwamnati na yi wa 'yan Najeriya da suka cancanta gwanjon kayan abincin da aka kama, musamman shinkafa, a kan farashi mai rahusa na N10,000 kowani buhu.
“Wasu daga cikin kayayyakin da za a sayar sun hada da buhuna 20,000 na hatsi iri-iri (Shinkafa, wake, masara, masara Guinea, gero, waken suya) buhunan kifi 963, busasshen barkono, tumatir, man girki, Maggi, taliyar Macaroni, gishiri, sukari da garin kwaki."

Kara karanta wannan

An debi garabasa: Jama'a sun mamaye 'dan kasuwa bayan da ya samar da shinkafa mai sauki, buhu N58k

Su wa za a siyarwa kayan abincin?

Adeniyi ya bayyana cewa domin cin gajiyar wannan kokari, dole ne mutum ya mallaki lambar shaida ta 'dan kasa (NIN), rahoton Vanguard.

Wadanda ake so su ci gajiyar wannan abu sun hada da 'yan Najeriya da ke zaune a yankunan da ake aiki wadanda suka hada da masu sana'ar hannu, malaman makaranta, malaman jinya, da kungiyoyin addinai.

Ya ce hukumar ta gindaya tsauraran matakai da ka'idoji don tabbatar da cewa mabukata ne kawai suka sami abubuwan.

Hukumar kwastam din ta kuma yi gargadi mai karfi kan sake siyar da kayayyakin cewa ta yi tanadi na musamman kan haka.

Dangote ya nesanta kansa da tsadar abinci

A wani labarin kuma, Aliko Dangote ya bayyana cewa babu sa hannun rukunoni kamfanonin Dangote a tsadar kayan abinci da ake fama da su a Najeriya.

Ta bakin Hajiya Fatima Aliko Dangote, babbar darakta a rukunonin kamfanin, Dangote ya ce shekara biyar kenan da ya sayar da kamfaninsa na sarrafa abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng