Tsadar Rayuwa: Matasa a Borno Sun Yi Barazanar Shiga Boko Haram, Bayanai Sun Fito
- Halin kunci a Najeriya ya fara sauya salo yayin da wasu matasa suka fito zanga-zanga a jihar Borno tare da yin barazana
- Matasan sun yi zanga-zanga kan halin kunci inda suka yi barazanar shiga kungiyar Boko Haram idan har ba a dauki mataki ba.
- Zanga-zangar ta barke ne a garin Dikwa da ke jihar kwana daya bayan ‘yan daba sun tare tirelar abinci a jihar Neja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno – Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, mazauna Dikwa a jihar Borno sun yi barazana ga gwamnati don kawo dauki.
Matasan sun yi zanga-zanga kan halin kunci inda suka yi barazanar shiga kungiyar Boko Haram idan har ba a dauki mataki ba.
Menene dalilin zanga-zangar a Borno?
Masu zanga-zangar suka ce basu iya ciyar da iyalansu saboda tsadar kayayyaki musamman kayan abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta tattaro daruruwan mata da yara ne suka fito zanga-zangar inda suka ce yunwa da kishirwa na neman hallaka su.
Wata majiya daga gwamnati ta ce Dikwa na fuskantar matsanancin karancin abinci dalilin hare-haren Boko Haram.
Har ila yau, wani mazaunin yankin ya ce halin da ake ciki ka iya jefa garin cikin matsi da zai lalata zaman lafiyar da aka samu a ‘yan shekarun nan.
Matsalar da aka samu a jihar Neja
Wannan barazana ta na zuwa ne yayin da jama’a ke cikin wani irin mawuyacin hali a kasar baki daya.
Har ila yau, a jihar Neja wasu matasa da ake zargin ‘yan daba ne sun farmaki tireloli dauke da kayan abinci tare da yin warwaso.
Lamarin ya tilasta sojoji bude wuta a jiya Alhamis 22 ga watan Faburairu a garin Sule da ke jihar Neja saboda halin kunci da ake ciki.
Wannan ya biyo bayan shan fama da ake yi a kasar bayan wasu tsare-tsaren tattalin arziki da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
Zulum zai rage farashin mai don manoma
Kun ji cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno zai samar da farashin mai cikin sauki ga manoma a jihar.
Gwamnan ya ce wannan mataki ya zama dole ganin yadda tsadar mai ke hana samar da kayan noma ga jama’a.
Asali: Legit.ng