Wahalar Rashin Albashin Wata 8 Ta Kashe Wasu Ma’aikatan Jami’a a Mulkin Buhari
- Gwamnatin tarayya ta biya malaman jami’o’in gwamnati da ke karkashin kungiyar ASUU albashin watannin da su ke bin bashi
- Kungiyoyin SSANU da NAAT sun ce dole ne a biya su kamar yadda aka yi wa malaman jami’o’i da su ne suka fara jawo yajin-aiki
- Malamai da yawa sun fadawa Legit an biya su, amma gwamnati tana neman hada fada a jami’o’in kasar a dalilin albashin da aka saki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Watanni bayan Bola Ahmed Tinubu ya canji Muhammadu Buhari, sai ga malaman jami’a suna farin ciki, an biya su albashin watanni.
Wani malamin jami’a da Legit ta zanta da shi ya tabbatar mata da an fara biyansu albashin watanni biyu, sai aka sake turo na watanni biyu.
Gwamnati ta biya 'Yan ASUU albashi
A cewar wani malamin jami’a, zai yi amfani da wadannan kudi ne wajen yin noma a shekarar nan, bayan ganin yadda abinci ya yi tsada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan ganin an biya bashin rabin kudin da suka dade suna sa rai, wani Farfesa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce sun yi murna.
Gwamnati za ta hada fada a jami'o'i
Duk da hobbasan da gwamnati tayi, sauran ma’aikatan jami’a sun koka cewa ‘ya 'yan kungiyar ASUU watau malamai kurum aka biya.
Mohammed Haruna wanda shi ne shugaban SSANU, ya shaidawa Vanguard cewa babu irin wahalar da ba su sha da aka daina biyansu ba.
Shugaban kungiyar manyan ma’aikatan jami’an ya ce ko da aka fara biyansu bayan an gama yajin-aikin, banki ne suka rika zaftare kudin.
Haruna ya ce yajin-aikin ya fi shafan SSANU saboda yawan ‘yan kungiyar, ya ce sun yi fama da rashin lafiya, kudin magani da gidan haya.
Abin da ya faru kuwa shi ne wasu ma’aikata sun karbi bashin banki da wahala tayi kamari, albashinsu suna fara shigowa, aka yi masu gibi.
...an sha wuya a jami'o'in gwamnati
Shugaban kungiyar NAAT, Ibeji Nwokoma ya fadi irin wahalar da suka sha a lokacin da aka rike masu albashi, ya ce wasu sun sheka barzahu.
NAAT tana ikirarin ma’aikata fiye da 50 wahala ta kashe da aka daina biyansu albashi, amma duk da haka gwamnati ta manta da su.
An biya ma'aikata N35, 000
Ana haka kuma sai gwamnatin tarayya ta biya ma’aikata bashin karin da ake yi duk wata, a makon nan aka biya kudin Nuwamba da Disamba.
Rahoto ya zo cewa gwamnatin Bola Tinubu tana shirin biyan ragowar N35, 000 da ta dauki alkawari za ta rika ba kowane ma’aikaci a wata.
An cin ma wannan yarjejeniya ne bayan cire tallafin fetur a Mayun bara, tsaida biyan kudin ya jawo NLC tana barazanar shiga yajin-aiki.
A lokacin da ASUU ta je dogon yajin-aiki a shekarar 2022, gwamnatin Najeriya ta tsaida albashinta, aka daina biyansu har watanni takwas.
Ganin malamai ba su shiga aji, gwamnati ta tado da dokar cewa babu aiki-babu albashi, hakan ya yi sanadiyyar da aka yi shari'a a kotu.
Asali: Legit.ng