Yajin Aikin ASUU: FG Na Iya Sauya Hukunci, Zata Biya Malamai Albashinsu da ta Rike

Yajin Aikin ASUU: FG Na Iya Sauya Hukunci, Zata Biya Malamai Albashinsu da ta Rike

  • Akwai yuwuwar gwamnatin tarayya ta biya malaman jami'o'i dake yajin aiki albashin watanni bakwai din su
  • Kamar yadda sakataren yada labarai na ma'aikatar ilimi ya bayyana, za a mika rahoton kwamitin duba bukatun malaman ga Buhari
  • Goong ya sanar da cewa, babu tabbacin za a duba matsalar UTAS daga kwamitin amma nan babu dadewa za a ji makomar malaman

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Ta yuwu gwamnatin tarayya ta sauya hukuncinta na kin biyan malaman jami'o'i masu yajin aiki albashinsu na watanni bakwai da suka gabata.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, ta yuwu gwamnati ta sake duba wasu daga cikin hukuncinta da ta yanke wadanda ASUU suka soka, lamarin da yasa malaman suka cigaba da yajin aiki duk da rokonsu da dalibai, iyaye da 'yan Najeriya ke ta yi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Kafa Kwamitin Da Zai Duba Bukatun ASUU

Minista Adamu Adamu
Yajin Aikin ASUU: FG Na Iya Sauya Hukunci, Zata Biya Malamai Albashinsu da ta Rike. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Gwamnatin a ranar Talata a wani taron iyayen jami'o'i da shugabannin jami'o'in suka yi, an kafa kwamitin mutum 14 wanda zai sake duba hukuncin kin biyan malaman albashi na tsawon lokacin da suke yajin aiki da kuam sauran matsalolinsu.

Daraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar ilimi, Bem Goong, ya zanta da manema labarai kan hukuncin da aka yanke yayin taron, yace kwamitin zai kara da duba manyan fannonin sannan a sake tattaunawa da ASUU.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Goong yace ba a tattauna kan matsalar tsarin biyan albashin malaman jami'o'in na University Transparency and Accountability Solution, UTAS ba, inda ya kara da cewa bata daga cikin abinda sabon kwamitin zai tattauna a kai.

Goong wanda bai bayyana tsawon lokacin da aka bai wa kwamitin don aikin da zai yi ba, yace za a mika rahoton abinda kwamitin ya cimma za a mika shi wurin shugaba Buhari a cikin kankanin lokaci.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

Buhari Ya Kafa Kwamitin Da Zai Duba Bukatun ASUU

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin da zai duba bukatun kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU.

Kungiyar ta fada yajin aiki tun daga ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kan farfado da jami'o'in gwamnatin, alawus dinsu da kuma amfani da tsarin UTAS wurin biyan albashin malaman da sauransu.

Ana tsaka da yajin aikin, gwamnatin ta kallafa dokar babu biyan albashi inda tace ba za ta biya malaman albashi ba a cikin watannin da basu yi aiki ba, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel