Jami'an 'Yan Sanda Sun Sheke Rikakken Mai Garkuwa da Mutane a Neja

Jami'an 'Yan Sanda Sun Sheke Rikakken Mai Garkuwa da Mutane a Neja

  • An rage mugun iri a jihar Neja bayan jami'an rundunar ƴan sandan jihar sun halaka wani mai garkuwa da mutane
  • Wanda ake zargin dai ya gamu da ajalinsa ne a wani artabu da ƴan ƙungiyarsa suka yi da jami'an ƴan sanda
  • Jami'an ƴan sandan a yayin artabun kuma sun ceto wata matashiya da miyagun suka yi garkuwa da ita bayan sun fatattake su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Neja a ranar Laraba sun kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a jihar.

Jami'ain ƴan sandan sun halaka wanda ake zargin ne a yayin wani artabu da suka yi bayan ya yi yunƙurin hana a cafke shi, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan jami'an tsaro sun yi kazamin artabu da 'yan ta'adda a jihar Arewa

'Yan sanda sun fatattaki masu garkuwa da mutane
Jami'an 'yan sanda a Neja sun yi nasara kan masu garkuwa da mutane Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Wanda ake zargin ɗan ƙungiyar wasu masu garkuwa da mutane mutum huɗu ne, sun yi wa wani ɗan kasuwa barazanar ya biya kuɗin fansa naira miliyan uku ko kuma su yi garkuwa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wanda ake zargin ya rasa ransa a hannun ƴan sanda, yayin da suka kuɓutar da wata matashiya mai shekaru 22 da aka yi garkuwa da shi.

Yadda ƴan sanda suka samu nasara

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairun 2024.

Kakakin ya ce rundunar ƴan sandan ta samu labarin cewa masu garkuwa da mutanen sun yi barazanar ne ga wani ɗan kasuwa a ƙauyen Bako-Mission na yankin Pissa a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar.

"Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Nan take bayan samun wannan bayanin, tawagar ƴan sanda ciki har da ƴan banga ƙarkashin jagorancin DPO na New-Bussa, suka garzaya zuwa wajen tare da yin artabu da masu garkuwa da mutanen.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace gawa da 'yan uwan mamacin, sun bukaci a ba su N50m

"Daga nan jami'an sun yi wa dajin ƙawanya inda suka kashe ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen a yayin artabun tare da ƙwato bindigarsa ƙirar AK-47 da jigida wacce babu komai a ciki.
"Sauran ƴan kungiyar sun tsere da raunuka daban-daban na harbin bindiga, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an cafke su."

Ƴan Sanda Sun Halaka Riƙaƙƙen Ɗan Daba

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an ƴan sanda a jihar Rivers sun halaka wani ƙasurgumin ɗan daba da ake nema ruwa a jallo.

Jami'an ƴan sandan sun halaka 2Baba ne a wani samame ta sama da ta ƙasa da suka kai a maɓoyarsa da ke cikin daji a ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng