"Guguwar AFCON Na Kadawa": Kyaftin Din Super Eagles, Ahmed Musa da Shehu Sun Ziyarci Sarkin Kano
- Har yanzu gwarazan kwallon kafa na kungiyar Super Eagles na ci gaba da haskawa kwanaki goma bayan gasar AFCON da aka yi a Ivory Coast a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu
- Ahmed Musa da mai tsaron baya, Shehu Abdullahi sun ziyarci mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero
- Dan wasan gefe na Sivasspor shi ne kyaftin din 'yan Super Eagles wadanda suka zo na biyu a gasar AFCON 2023 da aka kammala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Kano - Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa da mai tsaron baya, Shehu Abdullahi, sun kai ziyara ta musamman fadar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Wannan ziyarar na zuwa ne yan kwanaki bayan kungiyar Super Eagle ta sha kaye a wasan karshe na gasar cin kofin Afrika (AFCON) a Ivory Coast a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.
'Dan jarida Sulaiman Pooja Adebayo, ne ya wallafa hotunan a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter) @PoojaMedia, a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adebayo ya ce ziyarar da suka kai wa basaraken ya nuna cewa har yanzu guguwar AFCON na kadawa a Najeriya.
"Kyaftin din Super Eagles, @Ahmedmusa718 da tsohon mai tsaron baya, @OfficialShehu sun kai ziyara ta musamman fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
“Har yanzu guguwar AFCON na kadawa."
Jama'a sun yi martani
@dyk_footballng
"Sauran kasashe sun ci gaba da harkokinsu.
"Har ma da kasar da ta shirya da wadanda suka yi nasara sun ci gaba.
"Amma kun ga Najeriya mun cika son abu ya yi tsawo."
@simeon6239 ya ce:
"Har yanzu AFCON ce a sama."
muheezafo ya yi martani:
"Ya yi kyau."
@Kotachi_wins ya ce:
"Shugaban NFF na gobe."
Da gaske golan Ivory Coast ya daura guraye?
A wani labarin, mun ji cewa gasar cin kofin zakarun Afrika na AFCON ya kare a makon da ya gabata, inda kasar Ivory Coast ta yiwa Najeriya ci 2 da 1 a wasan karshe.
Sai dai, wasu da ke zuba ido a kafafen sada zumunta sun zargi cewa, akwai lauje cikin nadi a nasarar da kasar ta Ivory Coast ta samu.
Asali: Legit.ng