Yan Sanda Sun Kama ‘Sojojin Bogi’ a Legas, an Gano Abin da Zai Faru da Su

Yan Sanda Sun Kama ‘Sojojin Bogi’ a Legas, an Gano Abin da Zai Faru da Su

  • A ranar Laraba, rundunar 'yan sanda ta yi nasarar kama wasu mutum biyu da su ke ikirarin su sojojin Najeriya ne a jihar Legas
  • Tun da fari, rundunar ta samu rahoton yadda mutanen suka yi kokarin kashe wani mutum da wuka a kan titin Aina, Isolo da ke jihar
  • Bayan da aka kama mutane tare da bincikar su, an gano cewa sojojin boge ne, wadanda rundunar ta ce za ta gurfanar gaban kotu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu sojojin boge guda biyu wadanda ake zargin sun yi barazanar kashe wani mutum da wuka.

Kakakin rundunar na jihar, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da hakan a Legas ranar Laraba, ya ce wadanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda tun ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ta mamaye titunan Legas, bidiyon barnar da ruwan ya yi ya ja hankali

An kama sojojin bogi a Legas
Za a gurfanar da mutanen biyu gaban kotun da zaran an kammala bincike. Hoto: @LagosPoliceNG
Asali: Twitter

Hundeyin ya ce, rundunar ta Isolo a ranar Litinin da misalin karfe 10:30 na dare, ta samu labarin cewa ana yin artabu a titin Aina, unguwar Isolo a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce nan take aka tura tawagar ‘yan sintiri zuwa yankin domin kwantar da tarzoma da kuma bin ba'asi, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Za a gurfanar da mutanen biyu gaban kotu

Jami'in ya ce a lokacin da jami’an suka isa wurin, sun gano cewa wani Ben Okafor, ya yi ikirarin cewa shi kofur ne a rundunar sojojin Nijeriya, tare da wani Darlinton Ihenacho.

Hundeyin ya ce an ga mutanen biyu suna fada da wani Oludotun, wanda daga baya ya kai kara ga ‘yan sanda cewa wani soja yana binsa da wuka, yana barazanar kashe shi.

“Bayan an kama wadanda ake zargin tare da bincikar su, an same su da wani katin shaida na sojojin Najeriya na bogi, mai dauke da Cpl. Geoffrey Emmanuel, lambar aiki 140861.

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun cafke ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Kano

"Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu idan aka kammala bincike."

A cewar Hundeyin.

Yan sandan Legas sun kama dillalin ƙwaya dan shekara 67

A safiyar yau, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa rundunar 'yan sandan jihar Legas sun kama wani dattijo dan shekara 67 da ke sayar da kwayoyi a tintunan jihar.

An kama dattijon ne a lokacin da ya ke kokarin sayar wa wani yaro dan shekara 22 ƙwaya, a wani sumame da jami'an rundunar suka kai yankin Yaba da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.