Gwamnan PDP Ya Ɗau Zafi, Ya Dakatar da Fitaccen Basarake Daga Kan Karagar Mulki Saboda Abu 1

Gwamnan PDP Ya Ɗau Zafi, Ya Dakatar da Fitaccen Basarake Daga Kan Karagar Mulki Saboda Abu 1

  • Gwamnatin jihar Oyo karkashin shugabancin Gwamna Seyi Makinde ta dakatar da babban basarake na yankin ƙaramar hukumar Saki ta Yamma
  • Baale na Ilua ya rasa kujerarsa ne saboda zargin da hannunsa a rikicin da ya ɓarke tsakanin garuruwan Ilua da Gbepakan
  • Ma'aikatar ƙananan hukumomi da masarautu ta jihar Oyo ta ce an dakatar da shi ne domin kawo ƙarshen rikicin da kuma samun damar bincike na adalci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde, ta dakatar da Baale na Ilua da ke ƙaramar hukumar Saki ta Yamma, Cif Kilani Ajayi.

Kamar yadda jaridar The Nation ta tattaro, an dakatar da Cif Ajayi ne saboda wasu harkoki da yake gudanarwa waɗanda suka haifar da tashin hankali da fargaba a tsakanin al'umma.

Kara karanta wannan

Kujerar sakataren PDP na ƙasa ta fara tangal-tangal yayin da shugabanni suka faɗi wanda suke so

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Gwamnatin Oyo Ta Dakatar da Fitaccen Basaraken Gargajiya Daga Kan Mulki Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna ayyukan da basaraken ke yi sun haddasa rikici mai zafi tsakanin mazauna kauyukan Ilua da Gbepakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakatarwan da aka yi masa na kunshe a wata takarda mai ɗauke da adireshin kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu na Oyo, Olusegun Olayiwola.

Kwamishinan shari'a kuma Antoni Janar na jihar, Biodun Aikomo, ne ya aike wasiƙar dakatar da basaraken.

Ya bayyana cewa hukumar bunkasa harkokin ma’adanai ta Jihar Oyo ce ta bada shawarin dakatar da Cif Ajayi a wata wasiƙa da ta aika wa Antoni Janar.

Meyasa aka dakatar da basaraken?

Tuni dai ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu ta amince da wannan mataki domin daƙile yaɗuwar rikicin zuwa wasu kauyuka masu maƙotaka da garuruwan da abin ya shafa.

Haka zalika kuma dakatar da basaraken zai ba da cikakkiyar damar gudanar da bincike na adalci kan zarge-zargen da ake wa Cif Ajayi, Daily Post ta ruwaito

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fusata kan kisan babban jigo a APC, ya ba jami'an tsaro muhimmin umarni

Su wa suka shirya zanga-zanga a Oyo da wasu jihohi?

A wani rahoton na daban kun ji cewa Sanata Godswill Akpabio ya yi zargin cewa akwai wasu tsiraru a gefe da ke ɗaukar nauyin masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Shugaban majalisar dattawan ya ce mafi akasarin mutanen da ake amfani da su wajen zanga-zangar ba su san kokarin da FG ke yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel