Kalaman Akpabio Kan Emefiele Sun Jefa shi Cikin Babbar Matsala
- Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya yi wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, barazana kan ɓata masa suna
- Ta bakin lauyansa Emefiele ya buƙaci shugaban majalisar dattawa da ya nemi afuwa ko kuma ya fuskanci shari’ar ɓata suna ta naira biliyan 25
- Akpabio a ranar Lahadin da ta gabata ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gaji tattalin arziƙi wanda Emefiele ya lalata a lokacin yana gwamnan CBN
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya buƙaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya biya shi naira biliyan 25 a matsayin diyya, bisa zargin ɓata masa suna.
A ranar Lahadin da ta gabata, Akpabio ya ce zarge-zargen da ake yi wa Emefiele na da yawa wanda gwamnatin tarayya ba ta san irin tuhume-tuhumen da za ta yi masa ba.
Shugaban majalisar dattawa ya tona asirin masu ɗaukar nauyin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohi 4
Shugaban majalisar dattawan ya kuma ɗora laifin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar nan kan manufofin tsohon gwamnan na CBN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasikar mai ɗauke da kwanan watan 19 ga watan Fabrairu wacce jaridar TheCable ta gani a ranar Laraba, Emefiele ya aike da gargaɗi ga shugaban majalisar dattawan.
Me Emefiele yake buƙata a wajen Akpabio?
Matthew Burkaa, lauya ga Emefiele, ya ce idan Akpabio ya kasa biyan kuɗaɗen da aka ambata da neman yafiya, tsohon gwamnan na CBN zai ɗauki "matakin da ya dace", rahoton Leadership ya tabbatar.
A cewar lauyan, kalaman Akpabio na nuni da cewa Emefiele babban mai laifi ne wanda matakan da ya ɗauka su ne suka jawo wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki a halin yanzu.
Lauyan ya yi iƙirarin cewa maganar idan aka fassara ta a zahiri, tana nufin abu ɗaya ne, kuma hakan ya ɓata sunan wanda yake karewa, Emefiele.
Emefiele ya kuma bayyana cewa kalaman da Akpabio ya yi na kawo cikas ga gaskiya da ƴancin cin gashin kai na kotu kuma hakan na da illa ga shari’ar da ake yi masa a kotu.
An Bankaɗo Sabuwar Badaƙala a CBN
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta bayyana cewa an gano wasu kuɗaɗe da suka kai $8bn da aka fitar a bankin CBN.
Ƙungiyar ta ce Odita Janar na ƙasa ya umarci bankin CBN da ga fito ya yi bayanin kan dalilin da ya sanya aka fitar da kuɗaɗen.
Asali: Legit.ng