Ba a Gama da Emefiele Ba An Bankado Wata Sabuwar Badakala a CBN, Bayanai Sun Fito

Ba a Gama da Emefiele Ba An Bankado Wata Sabuwar Badakala a CBN, Bayanai Sun Fito

  • An fitar da sama da dala biliyan 8 [$8,973,684,257.95] daga asusun ajiyar Najeriya na ƙasashen waje tsakanin, 30 ga watan Yunin 2019 zuwa 30 ga watan Yunin 2020
  • Ƙungiyar SERAP ta ce an cire kuɗaɗen ne ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalilin da ya sa aka cire su ba
  • Ƙungiyar ta ce Odita janar na tarayya, Shaakaa Kanyitor Chira, ya umurci babban bankin Najeriya da ya yi bayani kan dalilin fitar da kuɗaden a wancan lokacin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa babban Odita Janar na tarayya, Shaakaa Kanyitor Chira, ya umurci babban bankin Najeriya (CBN) da ya yi bayani game da raguwar kuɗaɗe a asusun ajiyar ƙasashen waje na Najeriya.

Kara karanta wannan

Mai tsaron gidan Ivory Coast ya yi amfani da laya a wasan karshe na AFCON 2023

Kuɗaɗen dai ana zargin an cire su ne a tsakanin shekarar 2019 zuwa shekarar 2020.

An ba CBN sabon umarni
Odita Janar na son sanin dalilin cire kudade a asusun ajiya Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

Ƙungiyar SERAP ta ce an cire sama da dala biliyan 8 ($8,973,684,257.95) daga asusun ajiyar Najeriya na ƙasashen waje tsakanin 30 ga watan Yunin 2019 zuwa 30 ga watan Yunin 2020, ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne ta shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @SERAPNigeria, a ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu.

Ƴan Najeriya sun mayar da martani

@edoyakulo ya rubuta:

"Ɓacewar Dala Biliyan 8 daga asusun ajiyar waje ya kai kusan Naira Tiriliyan 12 a darajar yau, amma za a yi bayanin kuma ba wanda za a ɗaure."

@hannah_agha ta rubuta:

"Muna a cikin 2024 me yasa ba a yi binciken kafin yanzu ba"

Kara karanta wannan

Sa'o'i kadan bayan wani abun fashewa ya tashi, an sake samun mummunar gobara a Legas

@Peteraboh ya rubuta:

"A ƙarshe dai, ba za a yi wa kowa shari'a ba kuma ba wanda zai je gidan yari

@Tee_5806 ta rubuta:

"Buhari na buƙatar ya dawo ya amsa wasu tambayoyi."

@williamsidopise ya rubuta

"A lokacin da komai ya daidaita, za mu ga irin ɓarnar da Buhari ya yi wa tattalin arziƙin ƙasarmu. Ya kamata Tinubu ya gayyato Buhari da ƴan barandansa ko kuma za su ɗora laifin a kansa kamar yadda suke yi wa Emefiele."

SERAP Za Ta Maka Gwamnatin Tinubu a Kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta yi barazanar shigar da ƙara kan gwamnatin tarayya kan shirin sanya dokar amfani da shafukan sada zumunta.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa SERAP, ta ce manufar gwamnati ta saba da kundin tsarin mulkin ƙasa da ƙa'idojin kare hakkin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel