Bayan Yunwa Ta Nakasa Mutane, Gwamna a Arewa Ya Sake Fitar da Shinkafa Don Marasa Karfi, an Bi Tsari
- Gwamnatin jihar Kwara ta duba halin da mutane ke ciki inda ta yanke hukuncin sake raba shinkafa ga marasa karfi a jihar
- Sake rabon shinkafar za a yi ne ta amfani da shugabannin addinai da kungiyoyin NGO da sauran hukumomin unguwa
- Wannan na kunshe na cikin wata sanarwa da Hadimin gwamnan a bangaren ci gaban al’umma, Dakta Lawal Olohungbebe ya fitar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kwara – Yayin da ake cikin wani mugun yanayin tsadar rayuwa, gwamnatin jihar Kwara za ta fara rabon shinkafa.
Sake rabon shinkafar za a yi ta ne ta bangaren shugabannin addinai da kungiyoyin da ba na gwamnati ba wato NGO da sauran hukumomin unguwa.
Wane mataki gwamnatin Kwara ta dauka?
Wannan mataki na gwamnatin jihar an yi shi ne don rage wa jama’ar jihar radadi bayan cire tallafin mai da kuma tsadar rayuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin gwamnan jihar a bangaren ci gaban al’umma, Dakta Lawal Olohungbebe ya ce gwamnatin ta yi hakan ne don tabbatar da rabon ya isa ga jama’a.
Ya ce tabbas wadannan shugabannin addinai da kungiyoyin sun fi kusa da jama’a marasa karfi kuma sun san halin da suke ciki, cewar TVC News.
Tsarin da aka bi do rabon tallafin
A cewarsa:
“Mun yi imanin cewa wadannan kungiyoyi da malaman addini sun fi kusa da mutane kuma sun san yanayin da suke ciki.
“Har ila yau, sun fi kowa sanin wadanda suka fi bukatar tallafin a cikin al’ummar da suke rayuwa.
“Ta bangaren NGO kuma su na aiki ne da marasa karfi tuntuni wanda hakan zai taimaka wurin sanin mabukata.”
Hakan ya biyo bayan mawuyacin halin da ‘yan kasar suka shiga sakamakon tashin farashin kayayyaki musamman abinci.
Halin kuncin ya jefa mutane cikin mummunan hali wanda ya yi sanadin gudanar da zanga-zanga a wasu jihohi.
Sarkin Kano ya gargadi hukumar Kwastam
Kun ji cewa Sarkin Kano, Aminu Ado bayero ya shawarci hukumar Kwastam da ta bar ‘yan kasuwa su ci gaba da harkokinsu.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin da hukumar ke kama kayan ‘yan kasuwar da zargin su na fitar da shi waje.
Asali: Legit.ng