Gwamnati Ta Bayyana Ainihin Silar Mutuwar Gwamnan APC, Ta Fadi Babban Halin Gwamnan Na Kirki

Gwamnati Ta Bayyana Ainihin Silar Mutuwar Gwamnan APC, Ta Fadi Babban Halin Gwamnan Na Kirki

  • A karshe, gwamnatin jihar Ondo ta tabbatar da mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu bayan ya sha fama da jinya
  • Gwamnatin ta fitar da sanarwar ce awanni kadan bayan yaduwar rasuwar gwamnan a kasar Jamus
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinar yada labarai, Bamidele Ademola-Olateju ta fitar a yau Laraba 27 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Gwamnatin jihar Ondo ta bayyana asalin dalilin mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu a kasar Jamus a yau Laraba.

Gwamnatin ta tabbatar da mutuwar gwamnan awanni kadan bayan bullar labarin cewa gwamnan ya rasu, Legit ta tattaro.

Gwamnatin Ondo ta bayyana dalilin mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu
Gwamnati ta yi martani kan mutuwar gwamnan jihar Ondo. Hoto: Rotimi Akeredolu.
Asali: Facebook

Mene gwamnatin ta ce kan mutuwar Akeredolu?

Kara karanta wannan

Awanni kadan bayan shiga ofis, sabon Gwamna Lucky ya nada mukamai, ya yi wani gagarumin abu 1

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinar yada labarai, Bamidele Ademola-Olateju ta fitar a yau Laraba 27 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bamidele ta ce Akeredolu ya rasu ne a kasar Jamus a yau Laraba 27 ga watan Disamba bayan fama da cutar daji, cewar Premium Times.

Ta ce wannan rashi ya bar babban gibi a gwamnatin jihar da kuma zukatan mutanen jihar wadanda ke tare da shi lokacin da ya ke jinya.

Wace sanarwa gwamnatin ta fityar kan marigayin?

Sanarwar ta ce:

"Mai girma gwamna ya bar duniya cikin aminci a safiyar yau Laraba 27 ga watan Disamba.
"Mutuwar ta bar babban gibi a zukatanmu, Akeredolu ya amsa kiran Ubangiji a kasar Jamus.
"Ya rasu bayan fama da cutar daji, Akeredolu ba kawai gwamnan jihar Ondo ba ne illa mai burin ci gaban yankin Kudu maso Yamma da Najeriya baki daya."

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan jihar Ondo, Aiyedatiwa

Bamidele ta ce Gwamna Akeredolu mutum ne da ya ba da gudunmawa kwarai da gaske wurin ci gaban jihar baki daya.

Gwamna Lucky ya yi sabbin nade-nade

A wani labarin, Sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya yi sabbin nade-nade awanni kadan bayan hawa karagar mulki.

Lucky ya nada Ebenezer Adeniyan a matsayin sakataren yada labaransa da kuma wasu mukamai guda hudu.

Har ila yau, gwamnan ya ayyana hutun kwanaki uku don nuna alhini kan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Akeredolu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel