Sanatoci Sun Lalubo Yadda Gwamnatin Buhari Ta Haddasa Asarar Naira Tiriliyan 17
- Majalisar dattawa ta zauna da shugabannin hukumar FIRS a karkashin jagorancin Zach Adedeji a babban birnin tarayya watau Abuja
- Kwamitin kudi na majalisar ya koka game da tsarin afuwar haraji wanda ake zargin ya jawo an rasa N17tr da ya kamata su shiga baitul-mali
- Sanata Sani Musa yana Adedeji ya soke wannan tsari a FIRS ta yadda gwamnatin tarayya za ta iya samun harajin N30tr a shekarar nan ta 2024
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
FCT, Abuja - Kwamitin tattalin arziki na majalisar dattawa ya ce Najeriya ta rasa kusan N17tr a shekaru biyar da suka gabata.
Dalilin asarar wannan kudi kuwa kamar yadda Premium Times ta rahoto shi ne afuwar da ake yi wa wasu wajen biyan haraji.
Sanatoci sun yi zama da shugaban FIRS
Shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa ya bayyana haka a lokacin da ya tattauna da shugabannin hukumar FIRS a majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo tsarin da ya rika yi wa manyan kamfanoni afuwar haraji a kan dukiyar da suke samu.
Sanata Sani Musa mai wakiltar Neja ta gabas wanda ya soki yadda abubuwa suke tafiya, yana ganin an rasa kudin shiga ta tsarin.
Maganar Sanata Musa a kan tsarin Buhari
"Bayanan da ake da su sun nuna a shekaru biyar da suka wuce, kusan N17tr aka rasa a kasar nan a dalilin afuwar haraji."
"Ya kamata a dakatar da shi kuma a kawo sabon tsarin karbar haraji."
- Sanata Sani Musa
Ana so FIRS ta samu N30tr a 2024
Rahoton ya ce Sanatan ya yi kira ga shugabannin FIRS mai alhakin tattara haraja ta kara burin kudin da ta ke sa ran tatsowa a bana.
Idan babu wani kamfani da aka kebe wajen biyan haraji, Sanatan yana ganin kudin da za shigo cikin baitul-mali a 2024 za su karu.
Sabon shugaban na FIRS ya yi lissafin za su samu N19tr a shekarar nan, akasin N11tr da hukumar tayi hasashen za ta karba a 2023.
Za a yi watsi da shirin da Buhari ya kawo?
Business Day ta ce majalisar dattawa tana ganin idan aka dage za a iya samun N30tr.
Majalisar dattawan tana zargi ana son kai wajen yadda ake amfani da tsarin da aka kawo, saboda haka ake so Zach Adedeji ya soke shi.
Yaran Tinubu sun nemi karin hakuri
Ana da labari Folashade Tinubu-Ojo ta je wajen wani taron maulidi, a nan ta fadawa ‘yan Najeriya ba a kasar nan kadai ake wahala ba.
Yarinyar shugaban Najeriya ta ce a kara hakuri kadan, komai zai dawo daidai a mulkin Bola Ahmed Tinubu kamar yadda ake sa rai.
Asali: Legit.ng