Sojojin Saman Najeriya Sun Cafke Ƙasurgumin Mai Garkuwa da Mutane a Kano
- Rundunar sojin saman Najeriya (NAF), ta sanar da nasarar kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a jihar Kano
- Dakarun rundunar sun kama Isah Abdul wanda ke jagorantar wata daba da ta addabi wasu yankuna na jihar musamman Takai
- An ruwaito cewa tawagar Abdul ce ta yi garkuwa da Sarkin Noman Gaya da wasu 'yan mata 2 'yan gida daya da dai sauran su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Dakarun sojojin saman Najeriya da aka girke a Durbunde da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano sun kama wani babban mai garkuwa da mutane mai suna Isah Abdul.
An kama shi ne a ranar 19 ga Fabrairu, 2024 da misalin karfe 6:30 na yamma a wani sumame na hadin gwiwa bayan samun sahihan bayanan sirri.
Isah Abdul, fitaccen mai garkuwa da mutane ne da yaransa sun dade suna addabar yankin da ayyukan garkuwa da mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar sojin saman ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu, kuma rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook.
Ayyukan garkuwa da mutane da tawagar Abdul ta yi
AVM Gabkwet ya ce binciken farko ya nuna cewa Isah Abdul da ‘yan kungiyarsa ne suka yi garkuwa da wani Yakubu Ibrahim Tagaho.
"Sun yi garkuwa da Tagaho, wanda aka fi sani da "Sarkin Noman Gaya," a ranar 6 ga Afrilu, 2023, daga gidansa da ke kauyen Tagaho a karamar hukumar Takai.
"Bayan wata daya da yin garkuwa da Sarkin Noman Gaya, samu 'yanci bayan da tawagar Abdul ta karbi kudin fansa har naira miliyan 30."
- A cewar AVM Gabkwet.
Ya kara da cewar tawagar Abdul ta kuma yi garkuwa da wasu ‘yan uwa mata 2 da wasu mutum 3 a kauyen Tagaho, sun sake su bayan karbar makudan kudade.
Rundunar sojin na tuhumar Abdul a halin yanzu
AVM Gabkwet ya ce:
"Abdul na da alaka mai karfi da wasu sanannun kungiyoyin masu garkuwa da mutane kamar kungiyar Danbul Fulaku da ke gudanar da ayyukansu a karamar hukumar Takai."
Rahotannin sun bayyana cewa Isah Abdul a halin yanzu yana hannun rundunar sojin saman Najeriya, inda ake ci gaba da bincike,
Hakazalika nan ba da jimawa ba za a mika shi ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da shari’a.
Karanta sanarwar rundunar a nan kasa:
Mota ta murkushe barawon kayan abinci a kasuwar Abuja
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito yadda wani barawo ya so sace kayan abincin wata mata da ta siya, amma mota ta murkushe shi a Abuja.
Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talatar da ta gabata a kasuwar Kwali, inda aka karzaya da barawon asibiti ya yi raga-raga.
Matashin ya yi amfani da salon yaudara wajen karbar kayan abincin daga hannun matar, sai dai dubunsa ta cika lokacin da ya je callaka titi.
Asali: Legit.ng