Yajin Aikin Direbobin Tanka: Matashi Ya Koka Yayin da Ya Siya Fetur Kan N1,000 Lita a Jihar PDP

Yajin Aikin Direbobin Tanka: Matashi Ya Koka Yayin da Ya Siya Fetur Kan N1,000 Lita a Jihar PDP

  • Wani 'dan Najeriya ya garzaya dandalin soshiyal midiya don kokawa bayan ya siya man fetur kan N1,000 kowace lita daga wani gidan mai a ranar Litinin
  • Gidajen man fetur a fadin kasar sun rufe yayin da direbobin tanka suka janye kayayyakinsu a ranar Litinin domin zanga-zanga kan tsadar gudanar da aiki
  • Illar wannan yajin aiki shine ya dawo da layin man fetur sannan gidajen mai 'yan kadan da ke aiki sun kara farashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Yajin aikin direbobin tanka ya haddasa layion mai sannan gidajen mai 'yan kadan da suke da man fetur suna siyar da shi kan farashi mai tsada.

Wani 'dan Najeriya a dandalin X, Dr Donald Aniekwe, ya koka a soshiyal midiya bayan ya siya man fetur kan N1,000 kowace lita a Enugu a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Yadda wani mutum ya hallaka makwabcinsa saboda akuya, ya shiga hannun ‘yan sanda

Matashi ya koka da tsadar mai
Yajin Aikin Direbobin Tanka: Matashi Ya Koka Yayin da Ya Siya Fetur Kan N1,000 Lita a Jihar PDP Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Donald wanda ya kadu ya koka a shafin X:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ta faru ta kare! Yanzun nan na siya man fetur kan N1000/ltr."

Ya yada hoton da ya dauka daga gidan man da ya siya kaya don tabbatar da ikirarinsa, yana mai cewa ya shiga man ne a gidan mai na ChristNeky NG Ltd.

Wallafar da ya yi a Twitter ya jefa mutane da dama cikin kaduwa da rashin yarda.

Kafin ranar Litinin, 'yan kasuwar mai a kasar sun yi barazanar da dakatar da ayyuka kuma sun aiwatar da barazanar tasu.

Kalli wallafar Donald a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da matashi ya shiya mai N1000

@Ralphdani ya yi martani:

"N8000 kan lita 8.

"Idan muka shirya dai, za mu mamaye unguwanni sannan mu sauya lamarin kasar nan."

@hrh_nas ya ce:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun kashe masallata 3 tare da sace wasu da dama a jihar Arewa

"Yunkuri da ake yi da gangan don sa mutane su juyawa gwamnatin nan baya ba abin da za a yarda da shi bane. Dole mu hada hannu mu kula da wahalun da muke sha zuwa 'dan lokaci har zuwa san da abubuwa za su inganta.
"Ina da yakinin Baba yana aiki ba ji ba gani kasancewar baya bashi har sai karfe 2:00 na tsakar dare."

@lifemademe ta ce:

"Sai da na tabbatar da ganin cewa mahaifiyata ta mallaki na'urar solar kafin na tafi. Matsalar kawai shine yadda injinaya za su kula da ita koda ta samu matsala. Amma idan ba haka ba bata damu ba imma da wutar nepa ko babu."

@Therealchibiky ya ce:

"Don Allah fadi sunan gidan man, nima a Enugu nake kuma na siya 680, yayin da abokina ya siya 660 a gidan ban bovas sabuwar kasuwa."

Yadda wajen ibada ya zama gidan caji

A wani labari na daban, wani bidiyo da ke yawo a dandalin soshiyal midiya ya nuno wayoyi masu yawan gaske da aka jona jikin caji a wani wuri da aka ce coci ne.

A cewar @dahcutemide0, wacce ta wallafa bidiyon a TikTok, an dauki bidiyon ne a jami'ar Olabisi Onabanjo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng