Ana Karbar Kebura: Bidiyon Wani Matashi Da ke Shan Garin Kwaki da Man Ja Ya Girgiza Intanet

Ana Karbar Kebura: Bidiyon Wani Matashi Da ke Shan Garin Kwaki da Man Ja Ya Girgiza Intanet

  • Cece-kuce ya biyo bayan bidiyon wani matashi da ke yawo a dandalin soshiyal midiya inda aka gano shi yana shan garin kwaki da man ja
  • Abokin matashin ne ya kama shi yana tsaka da hada garin sannan ya dauke shi bidiyo cikin barkwanci don nunawa masu amfani da soshiyal midiya
  • Wasu mutane sun nuna aniyarsu na son taimakawa matashin da aka yi wa bidiyo, yayin wasu suka kalli abin da ya aikata a matsayin mai ban dariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani matashi 'dan Najeriya ya bar mutane cikin mamaki yayin da ya wallafa bidiyon abokinsa yana shan garin kwaki.

@olamilekandc009 ya yi wa abokinsa bidiyo sannan ya yada shi a dandalin TikTok, lamarin da ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a.

Kara karanta wannan

Tsadar siminti: Yadda wasu maza 2 suka dukufa ginin gida babu siminti, bidiyon ya haddasa cece-kuce

Matashi ya sha garin kwaki da man ja
Ana Karbar Kebura: Bidiyon Wani Matashi Da ke Shan Garin Kwaki da Man Ja Ya Girgiza Intanet Hoto: @olamilekandc009
Asali: TikTok

A cikin bidiyon, matashin ya zuba man ja a kan garin kwakin sannan yana shirin zuba ruwa ne sai ya lura da ana daukar abin da yake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nan take ya tsayar da abin da yake yi sannan ya boye garinsa da man jan a karkashin gado yayin da ya fashe da dariya.

Wannan bidiyo dai ya bayyana ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a fadin kasar, lamarin ya yi kamari har wasu iyali suna kwana da yunwa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun cika da mamaki

Tallbrownguy ya ce:

"Abin farin cikina shine idan har bai je ya roki wani ba toh ya kamata a daraja shi."

Makecash ya ce:

"Na yi wannan lokacin da nake karbar kebura baaba abin ba sauki fa oooo amma alhamdulillahi dai."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai kazamin hari kan matafiya, sun tafka mummunar ɓarna a jihar Arewa

omololadairo ya ce:

"Ka zo ka kara sikari ko gishiri abincin rana ya hadu kenan."

Bebonye ya ce:

"Ku nemo mani shi, ina so na albarkace shi da 500k."

sophia122405 ta ce:

"Me yasa kake yi masa bidiyo abin da za ku ci tare."

+86 ya ce:

"Da kunne nake ji cewa mutane na cin garin kwaki da mai ban taba gani ba ko sau daya."

oluwajuwonlohighman ya ce:

"Ku nemo shi ina so na ba shi 10k don ya siya kayan abinci."

An koma ginin laka saboda tsadar siminti

A wani labari na daban, mun ji cewa masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga wani bidiyo na wasu matasa biyu da ke gina gida ba tare da amfani da siminti ba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar siminti a fadin kasar wanda ya jefa 'yan Najeriya cikin wani yanayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng