“Tana Matukar Son Shi”: Bidiyon Wata Baturiya Da ke Matukar Son Garin Kwaki Ya Yadu

“Tana Matukar Son Shi”: Bidiyon Wata Baturiya Da ke Matukar Son Garin Kwaki Ya Yadu

  • Wata Baturiya da ke tsananin son shan garin kwaki ta yi fice a soshiyal midiya bayan an gano ta tana jin dadin abun a bidiyon TikTok
  • A cikin 'dan gajeren bidiyon, wani ya yi bayanin cewa tana son shan garin kwaki a kullun kuma cewa ta fi son shi fiye da abinci da aka girka
  • An gano Baturiyar tana jika gari tare da zuba sinadaren kara masa dadi kamar su madara, sikari da sauransu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar Baturiya da ke son shan garin kwaki kamar wata 'yan Najeriya ta dauka hankalin mutane a soshiyal midiya.

A cikin wani bidiyo da ya haifar da martani da dama a TikTok, an gano matashiyar tana jika garin kwaki cike da farin ciki.

Kara karanta wannan

AFCON" 'Dan Najeriya ya yi hasashen sakamakon wasan karshe tsakanin Najeriya da Ivory Coast

Matashiyar bata taba gajiya da shan gari
“Tana Matukar Son Shi”: Bidiyon Wata Baturiya Da ke Matukar Son Garin Kwaki Ya Yadu Hoto: TikTok/@mattieb28.
Asali: TikTok

An jiyo wata murya tana bayanin cewa matashiyar ta fi son shan garin kwaki fiye da abincin da aka girka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta jika garin kwakinta da sauran abubuwa da suka hada da madara sannan ta sha abin ta.

Bidiyon ya haifar da martani masu ban dariya, musamman a tsakanin 'yan Najeriya da suka gan shi a TikTok.

Wasu sun ce matashiyar na yin abu kamar wata 'yar Najeriya kuma cewa ya kamata a barta ta ji dadin rayuwarta. @mattieb28 ce ta yada bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Neojones phoncouch ya tambaya:

"Ina ruwan da ke cikin garin?"

@Sultan Süleyman Ikuforijimi ya yi martani:

"Shan garin kwaki da yawa yana illata idanu. Garin kwaki na da kyau amma kada a dunga shan sa da yawa."

@Maryam (Tays.Version):

"Cin busasshen garin kwaki laifi ne."

Kara karanta wannan

Bayan sace 'yan kai amarya, 'yan bindiga sun sake yin awion gaba da mutane a jihar Arewa

@Nezerduke ya ce:

"Baturiya take son Garin kwakinmu na Afrika da Najeriya? Wayyo Allah ina so na aureta."

@Chibuike ya ce:

"Da zaran ka fara shan garin kwaki, babu gudu babu ja da baya."

Garin kwaki ya hallaka wata yarinya

A wani labarin kuma, mun ji cewa yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa a fadin kasar, ibtila'i ya afkawa wasu iyali a jihar Kano inda ake zargin garin kwaki ya yi ajalin wata yarinya tare da galabaita yan uwanta su biyar.

Yarinyar mai suna Firdausi Mahmud Abdullahi ta kwanta dama bayan ta hambada garin kwaki a cikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel