Kano: Kotun Shari'ar Musulunci Ta Yi Hukunci Kan 'Yar Tiktok, Ramlat, Ta Fadi Dalilai

Kano: Kotun Shari'ar Musulunci Ta Yi Hukunci Kan 'Yar Tiktok, Ramlat, Ta Fadi Dalilai

  • Kotun Shari'ar Musulunci ta yi hukunci kan matashiyar 'yar Tiktok, Ramlat Muhammad a Kano kan wasu zarge-zarge
  • Kotun da ke zamanta a unguwar Sharada da ke jihar Kano ta tura Ramlat gidan gyaran hali kan zargin badala da yada karuwanci
  • Wannan na zuwa ne yayin da a daya bangaren ake ta cece-kuce bayan sakin Murja Ibrahim Kunya wacce itama aka gurfanar da ita

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kotun Shari'ar Musulunci da ke zamanta a jihar Kano ta yanke hukuncin dauri a gidan yari ga ’yar Tiktok, Ramlat Muhammad.

Kotun da ke zamanta a Unguwar Sharada ta yanke wa jarumar Tiktok din hukuncin ne kan samun ta da laifin yada badala da kuma karuwanci.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa aka fitar da Murja Kunya daga gidan gyaran hali, gwamnatin Kano ta magantu

Kotu ta tura Ramlat gidan gyaran hali kan wasu zarge-zarge
Kotun Shari'ar Musulunci ta tura Ramlat 'yar Tiktok gidan kaso. Hoto: Ramlat Muhammad.
Asali: Twitter

Mene ake zargin Ramlat da aikatawa?

Idan ba a manta ba, a ranar 19 ga Fabrairu ne Mai Shari’a, Sani Tanimu Hausawa ya yanke wa Ramlat hukuncin dauri na tsawon wata shida a gidan kaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ba ta zabin biyan tara kan laifukan da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta gurfanar da ita, cewar Aminiya.

An gurfanar da Ramlat kan wasu zarge-zarge da suka hada da laifin fitsara da rashin tarbiyya da yada badala a kafar Tiktok.

Sauran laifukan sun hada da yawon ta zubar da laifin fitsara wanda ya ci karo da sashe na 385.

Wasu zarge-zarge ake yi kan kan Ramlat?

Tun farko, alkalin ya yanke mata hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata uku ko zabin tara dubu talatin, cewar Daily News.

Har ila yau, sai tuhumar ta na yawon ba za wanda alkalin ya yanke mata hukuncin daurin wata uku a gidan gyaran hali ko zabin tara dubu ashirin.

Kara karanta wannan

FG Ta Yi Martani Kan Kirayen Tinubu Ya Yi Murabus Domin Wahalar Rayuwa, Bayanai Sun Fito

Sannan laifi na uku da aka kama ta da shi na laifin fitsara, ya yanke mata hukunci bisa sassauci da ta nema zaman gidan yari na tsawon wata daya babu zabin tara.

Kotu ta aike Ramlat a kurkuku

A baya, kun ji cewa Bayan sauraron korafin da aka shigar kan fitacciyar 'yar TikTok, Ramlat Mohammed, an tabbatar alkali ya garkame ta a gidan yari.

Rahotanni sun ruwaito cewa a ranar Juma'a 16 ga watan Fabrairu alkalin Kotun Musulunci ya yi umurnin tsare Ramlat Princess.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel