Ana Fama da Tsadar Rayuwa, Matsayin Murar Tebur Ta Fada Wata Jihar Arewa
- Rahotanni sun bayyana cewa an samu bullar cutar murar tsuntsaye a wasu sassa na jihar Kebbi kuma har ta kashe tsuntsaye a wata gonar kaji
- Cibiyar kula da cututtuka ta Jihar Kebbi (EOC) ta sanar da hakan inda ta bayyana cewa ta tuntubi hukumar lafiya ta duniya don dakile yaduwar cutar
- Daraktan sashen kula da dabbobi na EOC, Dr Alheri Ibrahim Senchi, ya ce kwayar cutar ta H5N1 na da matukar illa, wadda ka iya kai ga kashe mutane
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kebbi - Cibiyar kula da cututtuka ta Jihar Kebbi (EOC), ta sanar da jama’a game da bullar cutar murar tsuntsaye a wasu sassa na jihar.
Daraktan sashen kula da dabbobi na EOC, Dr Alheri Ibrahim Senchi, ya sanar da hakan a yankin Amanawa a karshen makon da ya gabata.
Dokta Senchi, ya ce an samun bullar cutar mai saurin kisa a cutar ne a wata gonar kaji da ke Amanawa, karamar hukumar Kalgo da ke jihar, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kebbi ta tuntubi hukumar lafiya ta duniya (WHO)
Ya ce barkewar cutar murar tsuntsayen da ta kashe duk dawisu da ke gonar kajin na da hatsari ga lafiyar dan adam kuma ta na iya kai ga kashe mutane.
Dokta Senchi ya ce an dauki matakan dakile cutar ta H5N1 cikin gaggawa don ganin ba ta bulla a fadin jihar ba.
A nasa bangaren, Daraktan kiwon lafiyar jama’a, Abubakar Bagudu, ya ce tuni cibiyar EOC ta gana da hukumar lafiya ta duniya (WHO) domin tabbatar da cewa cutar ba ta yadu ba.
Ya ce:
“Mun fito da wani tsari na daukar bayanan mutanen da suka yi cudanya da tsuntsayen tare da sa ido a kansu na tsawon kwanaki 14 don ganin ko za su kamu da wata cuta.
Wannan na zuwa ne yayin da kasar ke fama da tsadar rayuwa wanda ya shafi tsadar fetur, kayan masarufi da na abinci da tabarbarewar tattalin arziki.
Daurawa ya yi murabus daga shugaban Hisbah na Kano?
A wani labarin, Legit Hausa ta yi bincike kan jita-jitar da ke yadawa na cewar Mallam Aminu Daurawa ya yi murabus daga shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano.
A binciken da jaridar ta yi, ta gano cewa labarin ƙanzon kurege ne, domin malamin ko makusantansa ba su fitar da sanarwa kan murabus din ba a hukumance.
Ana fargabar cewa malamin ya yi murabus ne tun bayan da aka samu labarin Murja Kunya ta fita daga gidan gyara hali bayan da kotu ta ba da umarnin a tsare ta.
Asali: Legit.ng