Baya Ga Korona, Wata Sabuwar Cuta Ta Sake Bullowa a Kasar China Daga Kajin Gona

Baya Ga Korona, Wata Sabuwar Cuta Ta Sake Bullowa a Kasar China Daga Kajin Gona

- Hukumar lafiya a kasar China ta tabbatar da bullowar wata cuta daga dabbobi zuwa mutane

- Hukumar ta tabbatar da mutum na farko da ya kamu da cutar, wanda yake kwance a asibiti

- Hukumar lafiya ta duniya ta ce ba lallai cutar ta ke yaduwa tsakanin mutane cikin sauki ba

An tabbatar da wani mutum mai shekaru 41 a lardin Jiangsu da ke gabashin kasar China a matsayin mutum na farko da ya kamu da wani nau'in kwayar cutar murar tsuntsaye da ba a sani ba mai suna H10N3, in ji Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Beijing (NHC) a ranar Talata.

Jami'an hukumar ba su bayar da cikakken bayani game da yadda mutumin ya kamu da cutar ba amma ana tunanin cutar ta H10N3 ba za ta yadu cikin sauki tsakanin mutane ba, in BBC.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara Ya Tunkari Hedkwatar 'Yan Sanda Kan Dokar Harbe Masu Rike AK-47

An Kuma: Wata Sabuwar Cuta Ta Sake Bullowa a Kasar China Daga Kajin Gona
An Kuma: Wata Sabuwar Cuta Ta Sake Bullowa a Kasar China Daga Kajin Gona Hoto: reuters.com
Asali: UGC

Hukumar lafiyar ta ce mutumin, mazaunin garin Zhenjiang, an kwantar da shi a asibiti a ranar 28 ga Afrilu kuma ya kamu da cutar H10N3 a ranar 28 ga Mayu.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "a wannan lokacin, babu wata alama ta yaduwar cutar tsakanin mutum-da-mutum".

KU KARANTA: Daliban Islamiyya: 'Yan Bindiga Sun Magantu, Sun Ba Da Wa'adin Biyan Kudin Fansa

A wani labarin, A wani bidiyo da ya shahara a kafafen sanda zumunta, an ga wani mutum da ya yi ikirarin cewa ya auri aljana kana ya hada ta da matarsa mutum suke zaune a gida daya.

Mijin aljana, wato Malam Ahmadu Ali Kofar Na'isa, ya bayyana wasu abubuwan ban al'ajabi a baya, yayin da yake bayyana yadda yake mu'amalantar matarsa aljana duk da cewa halittarsu daban.

A wani bidiyon, har bayani ya yi na yadda yake cire kudade daga asusun ajiyar aljanu, wanda yake bashi damar cire kudaden Najeriya da wani katin ATM da yake dashi na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel