Tashin Hankali Yayin da 'Yan Bindiga Suka Farmaki Hedikwatar 'Yan Sanda a Zamfara, Bayanai Sun Fito
- Wasu ƴan bindiga sun kashe mutane a wani hari da suka kai garin Zurmi, hedikwatar ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara
- A ranar Lahadi, 18 ga watan Faburairu ne ƴan bindigan suka mamaye hedikwatar ƴan sanda da ke Zurmi inda suka yi ɓarna
- Ɗaruruwan mutane ne dai aka kashe a Arewacin Najeriya a hare-haren ta'addanci a a cikin ƴan shekarun nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Zurmi, jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun kai hari a hedikwatar rundunar ƴan sandan Najeriya da ke garin Zurmi, hedikwatar ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Kamar yadda jaridar Channels tv ta ruwaito, ƴan ta’addan sun mamaye garin ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Fabrairu, inda suka kashe mutane bakwai ciki har da ɗan sanda ɗaya.
Wani ɗan garin mai suna Babangida Zurmi ya bayyana cewa har yanzu bai yi magana da wani ɗan uwansa ba har zuwa ƙarfe 9:45 na dare saboda yawancin lambobinsu a kashe suke.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Yayin da muke magana yanzu, ba zan iya tuntuɓar kowa a garin ba, lambobin su a kashe suke. Hakan na nufin har yanzu ƴan bindigan na nan a wajen. Muna buƙatar taimako daga hukumomin da abin ya shafa."
Meyasa ƴan bindigan suka kai harin?
Wata majiyar kuma ta bayyana cewa ƴan bindigan sun kai hari garin ne da nufin ɗaukar fansa kan kisan da wasu ƴan banga da ke yankin suka yi wa abokan aikinsu mutum biyu.
A cewarsa, an ƙona shaguna da dama sannan an kuma ƙona hedikwatar ƴan sanda da ke Zurmi.
Wata ƙungiyar ƴan bindiga da ke aiki a ƙaramar hukumar Maradun ta kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da wasu da dama.
A cewar majiyoyi, mutane hudun sun mutu ne a lokacin da ƴan bindiga suka buɗe wuta kan mutanen da ke share ciyayi a kan hanya.
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar domin samun ƙarin bayani kan harin na garin Zurmi, sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba da safiyar yau Litinin, 19 ga watan Fabrairu.
Ƴan Bindiga Sun Halaka Mutane a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka mutum bakwai a wani hari da suka kai a ƙaramar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.
A yayin harin wanda suka kai a ƙauyen Nasarawa Godel, ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da kimanin mutum 20 daga ƙauyen.
Asali: Legit.ng