Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake komawa Kagara, sun bindige mutum hudu har lahira

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake komawa Kagara, sun bindige mutum hudu har lahira

- 'Yan bindiga sun sake kai hari a garin Kagara bayan sakin daliban GSS Kagara

- 'Yan bindigan sun yi sanadin rasuwar mutane hudu da suka bindige yayin harin

- Bata-garin sun kuma yi garkuwa da mutane 11, sun kuma sace shanu masu yawa

A kalla mutane hudu riga mu gidan gaskiya sakamakon sabon harin da yan bindiga suka kai garin Kagara a jihar Niger, Daily Trust ta ruwaito.

Garin Kagara ya yi fice tun ranar 17 ga watan Fabararun 2021 a yayin da tawagar yan bindiga dadi suka sace dalibai da ma'aiakata a GSS Kagara.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake komawa Kagara, sun bindige mutum hudu har lahira
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake komawa Kagara, sun bindige mutum hudu har lahira
Asali: Original

An sako wadanda aka yi garkuwa da su a yau sai kuma ga shi rahotanni sun bayyana cewa an kai sabon hari a Kagara.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Baku fi ƙarfin gwamnati na ba, Buhari ya gargaɗi ƴan bindiga

Majiyoyi daga Kagara sun shaidawa Daily Trust cewa an sace mutane 11 cikinsu akawai mata bakwai a wasu kauyuka biyu.

An ce yan bindigan sun kai hari a Gidan Adamu da ke kusa da Yakila, hedkwatar Gunna.

Kazalika, an kuma yi garkuwa da hakimin garin Yakila kuma har yanzu ba a gano inda ya ke ba.

Majiya ta shaidawa wakilin Daily Trust cewa yan bindigan sun kai hari a wani kauye mai suna Gidan Wamban Karaku inda suka sace mata bakwai ciki har da biyu masu shayarwa.

KU KARANTA: Bidiyon wani yana rushe gidan da ya gina wa budurwarsa saboda ta ce bata son shi

Sun kuma sace shanu masu yawa, a cewar majiyar.

Har ila yau, A yankin Madaka, sun yi garkuwa da limamin kauyen Rubo in ji majiyar.

A lokacin hada wannan rahoton, an riga an yi wa wadanda suka rasu jana'iza.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164