Kano da Kaduna Sun Shiga Jerin Jihohi 33 Da ’Yan Kasashen Waje Suka Ki Zuba Hannun Jarinsu
- Kimanin jihohi 33 na Najeriya ne suka gasa jawo hankalin masu zuba hannun jarin daga kasashen waje a cikin kwata na karshe na 2023
- Wani rahoto ya kuma bayyana cewa adadin jarin da aka shigo da shi Najeriya ya ragu ta hanyar gazawar jihohin
- Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, da Kogi ne ke kan gaba a jerin jihohin da suka gaza samun hannun jarin sama da dala biliyan 1.08
Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Najeriya - Jimillar darajar hannun jarin waje ko shigo da kudaden waje zuwa Najeriya ya kai dalar Amurka biliyan 1.08 a kwata na hudu na shekarar 2023.
Wannan yana wakiltar habaka zuwa 2.62% idan aka kwatanta da dala biliyan 1.06 da aka shigo dasu a matsayin hannun a kwata na hudu na 2022.
Hakanan, shigo da hannun jarin waje a kwatan karshe na 2023 wani babban ci gaba ne da 66.27% daga $654.65m a kwata na uku na 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga ina aka samu wadannan bayanai na hannu jarin 2023?
Wadannan alkaluma dai sun fito ne a cikin rahoton shigo da hannun jari na baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar a shafinta na intanet, rahoton The Cable.
Sai dai, duk da haka akwai jihohin Najeriya da suka fuskanci karancin hannayen jari daga kasashen waje saboda wasu dalilai.
Jihohin da suka dauki hankalin ‘yan kasashen waje har suka zuba hannayensu na jari a Najeriya sun hada da Legas, Abuja da kuma jihar Rivers, inji rahoton Vanguard.
Jerin da basu samu masu zuba jari ba a kwatan karshe na 2024
- Abia
- Adamawa
- Akwa Ibom
- Anambra
- Bauchi
- Bayelsa
- Benue
- Borno
- Cross River
- Delta
- Ebonyi
- Edo
- Enugu
- Gombe
- Imo
- Jigawa
- Kaduna
- Kano
- Katsina
- Kebbi
- Kogi
- Kwara
- Nasarawa
- Niger
- Ogun
- Ondo
- Osun
- Oyo
- Plateau
- Sokoto
- Taraba
- Yobe
- Zamfara
Jihohin da aka fi tsadar gas din girki a Najeriya
A wani rahoton, NBS ta fitar da jerin jihohin da aka fi samun tsadar gas din girki a Najeriya, inda da aka bayyana su dalla-dalla.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kuka kan yadda kayayyaki suka yi tsada, musamman bayan janye tallafin man fetur.
Sai dai, duk da haka, gwamnati na ci gaba da cewa tana kokarin tabbatar da an samu sauki wajen inganta rayuwar ‘yan kasar.
Asali: Legit.ng