Tsadar Rayuwa: Gwamnonin PDP Sun Nemi Tinubu Ya Yi Murabus, Sun Fadi Dalili
- Gwamnonin jam'iyyar PDP sun nemi shugaban kasa Bola Tinubu na jam'iyyar APC da ya yi murabus daga shugabancin Najeriya
- Wannan kiran ya biyo bayan tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta kamar yadda kungiyar gwamnonin PDP ta bayyana
- A cewar kungiyar, Najeriya ta shiga mawuyacin hali tun bayan da APC ta hau mulki a 2015, don haka akwai buƙatar ta hakura da mulkin gaba daya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Gwamnonin jam'iyyar PDP sun nemi gwamnatin jam'iyyar APC da ta yi murabus daga mulki idan har ba za ta iya magance tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar ba.
Sanin kowa ne cewa an samu hauhawar farashin kayan abinci da tabarbarewar tattalin arziki wanda ya jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali, a cewar gwamnonin, rahoton Vanguard.
A ranar Litinin da ta gaba, gwamnonin PDP karkashin Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, sun ce Najeriya na dab da komawa Venezuela a ƙarƙashin mulkin Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu ta ki daukar shawarwarin PDP
Sai dai ministan watsa labarai, Mohammed Idris ya yi martani da cewa gwamnonin PDP ne suka jawo matsin rayuwar saboda gaza biyan albashi, giratuti da fansho a jihohin su.
Amma a ranar Asabar, darakta janar na kungiyar gwamnonin PDP, Cyril Maduabum, ya shaida cewa babu irin shawarar da gwamnonin ba su ba gwamnatin tarayya ba amma aka ki amfani da su.
Ya ce shawarwarin sun shafi yadda za a magance matsalolin tsaro, tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da ke addabar kasar.
Duk da hakan, kungiyar ta yaba wa Tinubu kan ganawa da gwamnoni domin magance manyan matsalolib da kasar ke fuskanta.
PDP za ta taya Tinubu shawo kan matsalolin Najeriya
Ya ce:
"Tsadar rayuwa ba ruwan ta da addini, kabila ko banbancin jam'iyya, duk mayunwacin mutum za a same shi mai yawan fushi, don haka dole a kawo sauki wa al'umma.
"Ma damar gwamnatin tarayya mai ci a yanzu ba za ta iya magance matsalolin tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki ba, to kawai ta hakura da mulkin ta ba wasu wuri."
Daraktan kungiyar ya kuma jaddada cewa jihohin da PDP ke mulki sun fi ko ina tsare tsare masu kyau kuma ana biyan albashi akan kari.
Ya ce gwamnonin PDP za su gaba da aiki da shugaban kasa wajen ganin an shawo kan matsalolin da APC ta jefa kasar tun bayan hawa mulki a 2015.
Tsadar rayuwa: Ba laifin Tinubu ba ne, a cewar Igboho
A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito yadda mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya caccaki kalaman Sarkin Musulmi kan tsadar rayuwa.
Igboho ya ce akwai rashin adalci a kalaman mai martabar da ke nuna cewa an shiga tsadar rayuwar ne a mulkin Tinubu har yana gargadin hukumomin kasar kan halin da kasar ke ciki.
Sunday Igboho ya ce bai kamata tun yanzu a fata dora laifin halin da kasar ta shiga akan gwamantin Tinubu ba saboda ba ta yi wa'adin shekara daya a mulki ba.
Asali: Legit.ng