“Sun Rasa Muryarsu Karkashin Buhari”: Shehu Sani Ya Magantu Yayin da Sarakunan Arewa Ke Sukar Tinubu

“Sun Rasa Muryarsu Karkashin Buhari”: Shehu Sani Ya Magantu Yayin da Sarakunan Arewa Ke Sukar Tinubu

  • A 'yan kwanakin nan, shugabannin Arewa musannan sarakuna sun nuna rashin jin dadinsu da manufofin Tinubu wanda ya haddasa yunwa da wahalhalu a kasar
  • Da yake martani, Sanata Shehu Sani ya yi adawa da sukar gwamnatin Tinubu da sarakunan gargajiyan ke yi
  • Tsohon 'dan majalisar tarayyar ya yi mamakin dalilin da yasa suke iya sukar gwamnatin Tinubu amma suka yi gum lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi Allah wadai da sukar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Bola Tinubu da sarakunan Arewa ke yi saboda matsin rayuwar da 'yan Najeriya ke fuskanta.

Legit Hausa ta rahoto a baya cewa shugaban, majalisar sarakunan gargajiya na Arewa kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar lll ya ce Najeriya na dane ne kan bam.

Kara karanta wannan

Aiki na Kyau: Dalilin Shugaba Tinubu na ware Abba, ya jinjina masa cikin Gwamnoni

Shehu Sani ya yi shagube ga sarakunan Arewa
“Sun Rasa Muryarsu Lokacin Buhari”: Shehu Sani Ya Magantu Yayin da Sarakunan Arewa Ke Sukar Tinubu Hoto: Senator Shehu Sani, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sarkin ya bayyana cewa rashin aikin yi da yunwa da ke kasar ba karamar matsala ba ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sultan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 14 ga watan Faburairu a Kaduna yayin taron sarakunan gargajiya a Arewa.

Hakan na zuwa ne bayan Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta sanar da mijinta halin da 'yan Najeriya ke ciki a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu.

Da yake martani ga ci gaban, tsohon dan majalisar tarayyar, Sani a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X ya zargi sarakunan Arewa da bangaranci.

Sani ya yi mamakin dalilin da yasa sarakunan gargajiyan suke iya magana a gwamnatin Tinubu amma suka yi shiru lokacin da abubuwa suka tabarbare a mulkin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Muhimman matakai 6 da aka dauka da Tinubu ya zauna da Gwamnoni a Aso Villa

Jigon na PDP ya ce:

"Tsawon shekaru takwasa, Sarakunan gargajiya daga Arewa sun rasa muryarsu a karkashin Buhari; sun nemo ta a yanzu."

Ganduje ya magantu kan tsadar rayuwa

A wani labarin, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen da ta ke fuskanta.

Ganduje ya bayyana cewa hakan zai faru ne idan aka yi duba da irin matakan da ake ɗauka na baya-bayan nan, don shawo kan matsalolin, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng