Muhimman Matakai 6 da Aka Dauka da Tinubu Ya Zauna da Gwamnoni a Aso Villa
- Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da gwamnoni a kan halin tsadar rayuwar da mutane suka shiga a Najeriya
- Gwamnonin jihohi da yawa sun halarci taron da aka yi a fadar Aso Rock tare da Kashim Shettima a garin Abuja
- Shugaban Najeriyan ya yi kira na musamman ga gwamnoni domin a magance tsadar farashi da wahalar abinci
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya hadu da gwamnonin jihohin Najeriya a game da halin kuncin rayuwar da al’umma su ka shiga.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya na cikin wadanda aka yi zaman da su kamar yadda Punch ta kawo rahoto.
Haduwar Tinubu da Gwamnoni a Aso Rock
Baya ga gwamnoni, Nyesom Wike yana wajen taron a matsayinsa na Ministan Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi zaman ne a fadar shugaban kasa na Aso Rock Villa da ke Abuja da korafi ya fara yawa kan tsadar rayuwa da wahalar abinci.
Temitope Ajayi ya fitar da gajeren jawabi a shafinsa na X bayan zaman da aka yi dazu.
Mai taimakawa shugaban kasar ya bayyana jeringiyar matakan da aka cin ma bayan wannan zama na musamman da aka yi dazu.
Jawabin ya samu sa hannun mai taimakawa shugaba Bola Tinubu wajen yada labarai da kuma dabaru watau Mista Bayo Onanuga.
Matsayar zaman Tinubu v Gwamnoni
1. Inganta tsaro
Za a bukaci daukar karin ‘yan sanda domin shawo kan matsalar tsaro wanda hakan ya kawo matsala wajen noman abinci a kasar.
Za a hada-kai da ‘yan majalisar tarayya domin kafa ‘yan sanda a matakin jihohi a madadin jami’an sa-kai da gwamnoni su ke kirkira.
2. Tsadar abinci
Bola Tinubu ya soki yadda ake boye abinci kuma ya ce a maida hankali ga noma, ya yi gargadi a kan bude iyakoki domin kawo abinci.
3. Boye abinci
Shugaban kasa ya ba gwamnoni shawara suyi koyi da Abba Kabir Yusuf, kuma zai kafa kwamiti da zai yi maganin masu boye kayan abinci.
4. Inganta noma
Jawabin ya ce shugaba Bola Tinubu ya kuma bukaci gwamnoni su maida hankali a sha’anin kiwo musamman kiwon dabbobi da kifi a jihohi.
5. Albashi
Ajayi ya shaidawa Najeriya an nemi gwamnoni su rika biyan hakkokin ma’aikata kan kari, musamman tun da kudin da ake samu a FAAC ya karu.
6. Dabarun tattalin arziki
A karshe an yi kira ga gwamnatocin jihohi su fito da dabarun samun kudi, kuma a tabbata matasa sun samu abin yi, a daina zaman banza.
Bola Tinubu zai fuskanci kalubale
Baya ga wahalar rayuwa, kungiyoyin ‘yan kwadago su na barazanar shiga yajin-aiki saboda zargin gwamnati da saba alkawarin da ta dauka.
Tsofaffin ma’aikata sun shirya za su yi zanga-zanga tsirara saboda rashin biyansu fansho wanda hakan ya hurowa gwamnatin kasar wuta.
Asali: Legit.ng