NMDGIFB: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Wani Muhimmin Nadin Shugaba Tinubu

NMDGIFB: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Wani Muhimmin Nadin Shugaba Tinubu

  • Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin Adama Oluwole Oladapo a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan samar da iskar gas (NMDGIFB)
  • Shugaba Bola Tinubu ne ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Oladapo kamar yadda dokar kafa NMDGIFB ta tanada
  • Har ila yau, a ranar Alhamis, majalisar dattijai ta yi jumamin mutuwar marigayi Asagba na Asaba, Obi Chike Edozien are da yin shiru na minti

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Majalisar dattijai ta tabbatar da nadin sabon babban darakta na hukumar kula da ayyukan samar da iskar gas ta Najeriya (NMDGIFB).

Adama Oluwole Oladapo shi ne wanda majalisar ta yarda da nadin sa a ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, domin shugabantar NMDGIFB.

Kara karanta wannan

Bayan CBN da FAAN: Gwamnati na shirin dauke hukumar NUPRC daga Abuja zuwa Legas

NMDGIFB: Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Adama Oladapo
NMDGIFB: Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Adama Oladapo kamar yadda Tinubu ya bukata. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

The Nation dai shugaba Bola Tinubu ne ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Oladapo kamar yadda dokar kafa NMDGIFB ta tanada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta amince da nadin biyo bayan shawarar kwamitin kula da albarkatun iskar gas da man fetur (Dowstream) ta bayar bayan da ya tantance Oladapo, NTA ta ruwaito.

Majalisar ta yi jumamin mutuwar Sarkin Asaba

Wannan nadin na zuwa jum kadan bayan da hukumar da ke sa ido kan man fetur da iskar gas a Najeriya (NUPRC) ta sanar da shirin mayar da wasu sassa na hukumar zuwa Legas.

Har ila yau, a ranar Alhamis, majalisar dattijai ta yi jumamin mutuwar marigayi Asagba na Asaba, Obi Chike Edozien, tare da yin shiru na minti daya don karrama shi.

Hakan ya biyo bayan wani kudiri da Sanata Ned Nwoko (PDP – Delta North) ya gabatar a zauren majalisar wanda ya ja hankalin abokan aikin sa kan rasuwar sarkin Asaba.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

Babban basarake a Najeriya, Joseph Edozien ya kwanta dama

Tun da farko, Legit Hausa ta kawo maku labarin cewa mai martaba Sarkin Asaba, Farfesa Joseph Chike Edozien ya rigamu gidan gaskiya.

Mai martaba Edozien ya rasu ne a makon da ya gabata a yayin da ya ke shirye-shiryen bukin cika shekara 100 a duniya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mutuwar ta Edozien ta kawo lissafin sarakunan Asaba da suka mutu akan karagar mulki zuwa mutum 13.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.