Hukumar Hisbah Ta Aikawa ‘Yan Iskan Gari Sako da Aka Rufe Murja Kunya a Kurkuku

Hukumar Hisbah Ta Aikawa ‘Yan Iskan Gari Sako da Aka Rufe Murja Kunya a Kurkuku

  • Hisbah za ta koyawa masu shakiyanci a Tik Tok darasi bayan an dauki mataki a kan Murja Kunya
  • Hukumar da ke yaki da alfasha a Kano za ta fara gurfanar da masu tallata badala a gaban alkalai
  • Ganin duk wani nau’i na lallashi da jan hankali bai yi tasiri ba, Hisbah za ta canza salo a Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano tayi karin haske a game da matakin da aka dauka a kan Murja Ibrahim Kunya.

Wannan bayani ya fito ne ta bakin Dr. Khadijah Sulaiman wanda tana cikin mataimakan shugaban hukumar Hisbah.

Hukumar Hisbah'
'Yan Hisbah a Kano Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Karshen Murja Kunya ya zo?

Dr. Khadijah Sulaiman ta zanta da ‘yan jarida a ranar Talata, ta ce lokaci ya yi da za a hukunta Murja Kunya a dalilin aikinta.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya fadi masifar da za ta faru idan ba a dauki mataki ba, akwai dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakiyar shugabar ta sashen mata ta ce Hisbah ta dade ta na bin mataki na ruwan sanyi a kan ‘Yan Tik Tok din.

Sheikh Aminu Daurawa ya zauna da masu aiki da dandalin Tik Tok, ya ja hankalinsu a kan yin ayyukan badala a shafinsu.

Hisbah ta zo da sabon salo a Kano

Ganin wa’azi da jan-hankali bai yi tasiri ba, Khadijah Sulaiman ta ce sai aka kai zancen kotu domin alkali ya yi hukunci.

Jagorar ta ce da zuwan gwamna Abba Kabir Yusuf, sun bi sababbin dabaru, ta kuma ce ba za su bari a cigaba da barna ba.

Jawabin shugabar Hisbah ta mata

"Ni ba Alkaliya ba ce, amma na san a wannan gwamnati, ba za a kyale wannan abin haka sakaka ba."
"Na tabbata abin nan ya zo karshe da yardar Allah SWT."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

"Ai na fada masu, nasiha na ke yi masu. Dukkan wata mai yin badakala a Tik Tok ta shiga taitayinta."
"Mun tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro. Saboda haka kowace mace da ta ke shirin badala kuma ta fito da shi a fili, hukumar Hisbah ba za ta amince ba, kuma za ta dauki matakin da ba zai yi masu dadi ba."

- Dr. Khadijah Sulaiman

Hisbah tayi kira ga al'ummar Kano

An ji labari Hisbah ta bada shawarar a rika amfani da dandalin zamanin wajen sada zumunta a maimakon a rika yada alfasha.

Ga masu yin aika-aika kuma su fito da shi fili, Hisbah ta ce ta tanadi karfafan mata da za su iya cafko duk wata maras kunya a Kano.

A sanadiyyar wannan kokari ne aka rufe asusun da hukumar ta ke da su a bankuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng