Sanata Marafa Ya Yi Barazanar Maka Sabuwar Rundunar Tsaron Jihar Arewa a Kotu Kan Dalili 1
- Sanata Kabiru Marafa ya magantu bayan mutuwar wani na hannun damarsa, Alhaji Magaji Lauwali, wanda ake zargin jami'an tsaro da hallakawa
- Tsohon 'dan majalisar tarayyar da ya nuna fushinsa, ya yi barazanar daukar tsatsauran mataki a kan sabuwar rundunar tsaro ta CPG a jihar Zamfara
- Marafa ya zargi rundunar tsaron da azabtar da abokinsa da wani har sai da shi Magaji ya rasa ransa kan haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Sanata Kabiru Marafa ya yi bazanar daukar mataki na doka kan wasu jami'an rundunar tsaro da aka kaddamar kwanan nan a jihar Zamfara.
Tsohon 'dan majalisar tarayyar ya yi barzanar maka rundunar CPG a kotu ne kan kisan abokinsa a siyasa, Alhaji Magaji Lauwali, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Babban lamari ya faru bayan mata ta yi ajalin makwabciyarta da wuka kan wani dalili, an rasa ta cewa
Yadda jami'an CPG suka azabtar da abokina har ya mutu- Marafa
Da yake jawabi ga taron manema labarai a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, Sanata Marafa ya yi zargin cewa Lauwali ya mutu ne a hannun rundunar CPG a ranar Lahadi bayan jami'anta sun yi masa horo mai tsanani a yankin Tsafe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce rundunar CPG ta gayyaci marigayi Magaji da wani mutum daya zuwa ofishinsu inda suka azabtar da su, rahoton Daily Post.
Sanata Marafa ya ce:
“An azabtar da su biyun sosai, yayin da daya mutumin ya tsira daga azabar dauke da raunuka a kafadunsa biyu, Magaji ya rasu watakila saboda munanan raunukan da ya samu a bangaren jikinsa na hagu.
"Yana ta zubar da jini ta hanci, idanu da baki. Mun lura da alamun jini a gaba daya fuskarsa.”
Ya ce ya bayar da umarnin yi wa gawarsa gwaji sannan an tura gaba daya bayanan kira da ke wayar mnamacin zuwa ga kamanonin sadarwar don gano wadanda ke da hannu a lamarin Magaji.
Ya kuma ce duk wadanda aka samu da hannu a kisan sai sun fuskanci hukunci na doka.
Me mahukunta suka ce?
Har wayau, Marafa ya ce DPO na Yandoto ya tabbatar masa da cewar ba a sanar masa da batun kamun ba sannan cewa ba a sanar da masarautar ba ma.
Sanata Marafa ya yi zargin cewa rundunar ta CPG ta kuma tsare 'dan uwa da yaron marigayin, Babani da Nura, bayan sun je oishinsu don karbar wayar marigayi Magaji.
Ya koka:
"An azabtar da mutanen biyu sannan aka tursasa su bayar da jawabi bayan jami'in CGP ya karbi bayanan nasu, sai suka turasasa su sanya hannu akan takardun."
Gwamnatin Zamfara ta dau mataki
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta umurci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan zargin arangama tsakanin jami'an rundunar CPG da wasu 'yan haramtacciyar kungiyar 'Yansakai a yankin Tsafe wanda ya kai ga mutuwar mutum daya.
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar M Nakwada ya fitar, ya bayyana cewa gwamnati na sane da rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu, yana mai tabbatar da cewa an shawo kan lamarin.
Gwamnatin Zamfara ta dauki mataki kan tsaro
A wani labarin, gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da hana sayar da biredi da man fetur a jarkoki ga masu motoci da masu tuƙa babura saboda dalilai na tsaro.
Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mannir Muazu Haidara ya bayyana haka a taron manema labarai a ƙarshen taron majalisar tsaro na jihar, cewar rahoton PM News.
Asali: Legit.ng