Yayin da Ya Fara Hucewa Kan Rashin Nasarar Super Eagles, Tinubu Zai Shilla Wata Kasa, an Fadi Dalili

Yayin da Ya Fara Hucewa Kan Rashin Nasarar Super Eagles, Tinubu Zai Shilla Wata Kasa, an Fadi Dalili

  • Kwanakin kadan bayan dawowa daga Faransa, Bola Tinubu zai sake tafiya kasar Habasha don halartar babban taro
  • Tinubu zai tashi ne a gobe Alhamis 15 g watan Faburairu don halartar taron da za a yi a birnin Addis Ababa a karo na 37
  • Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya sanar da haka a yau Laraba 14 ga watan Faburairu a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu zai tafi kasar Habasha don halartar babban taron kungiyar Nahiyar Afirka (AU).

Tinubu zai tashi ne a gobe Alhamis 15 g watan Faburairu don halartar taron da za a yi a birnin Addis Ababa a karo na 37.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da jami'an tsaron Najeriya suka dauka don kama 'yan ta'adda cikin sauki

Yayin da ake cikin wani hali, Tinubu zai sake barin Najeriya
Tinubu zai tafi kasar Habasha don halartar babban taro. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu zai bar Najeriya?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Laraba 14 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ngelale ya ce Tinubu zai gana da sauran shugaban kasashen don tattauna kawo sauye-sauye a kungiyar.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai tafi birnin Addis Ababa da ke Habasha a gobe Alhamis 15 ga watan Faburairu.
"Tinubu zai gana da sauran shugabannin kasashen Afirka a karo na 37 don kawo sauye-sauye a kungiyar.

Yaushe Tinubu zai dawo Najeriya?

Ngelale ya ce taron wannan karon zai mai da hankali ne wurin inganta ilimi da koyarwa a Nahiyar Afirka.

Tinubu zai samu rakiyar wasu daga cikin Ministoci da jiga-jigan gwamnati inda ake sa ran dawowarsa da zarar an kammala taron.

Wannan tafiya na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban ya dawo daga kasar Faransa don hutu na kwanaki.

Kara karanta wannan

NNPP ta yadu zuwa wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

Jami'yyar PDP ta shirya taimakon APC

Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta shirya yin adawa mai amfani madadin kushe tsare-tsaren gwamnati.

Jami'yyar ta ce a yanzu ana cikin wani hali na kunci tattalin arziki wanda ya hana mutane sakat.

Wannan mataki na jam'iyyar PDP na zuwa ne yayin da ake cikin wani hali a kasar na mawuyacin hali da tsadar kayayyaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.