Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Daba Suka Hargitsa Zaben Cike Gurbi da INEC Ke Gudanarwa a Jihar Enugu
- Wasu 'yan daba sun kai farmaki wuraren da ake gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Enugu ta Gabas da ke jihar Enugu
- Hukumar INEC ce ta sanar da hakan a shafinta na X a ranar Laraba, inda ta ce 'yan dabar sun lalata kayayyakin zaben gaba daya
- A hannu daya kuma INEC ta ce tana ci gaba da gudanar da zabe a kananan hukumomi uku na jihar Taraba, kuma zaben na tafiya dai dai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Enugu - Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta ce wasu 'yan daba sun hargiza zaben cike gurbi da jami'an hukumar ke gudanarwa a jihar Enugu.
Idan ba a manta ba, kotu ce ta ba INEC umurnin gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Enugu ta Kudu a majalisar jihar.
INEC ta fitar da sanarwar farmakar jami'anta a Enugu
Hukumar a shafinta na X a ranar Laraba ta ce 'yan dabar sun lalata dukkanin kayayyakin zabe amma babu wanda aka ji wa rauni daga farmakin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta ce:
"Ofishin hukumar mu na jihar Enugu ya sanar da mu cewa wasu 'yan daba sun hargitsa zaben da ake yi a mazabar Enugu ta Gabas.
"Tuni jami'an mu suka bar wajen ta hanyar samun taimako daga jami'an tsaro."
Zaben cike gurbi a jihar Taraba na gudana cikin kwanciyar hankali
INEC ta kuma shaida cewa zaben da take gudanarwa a mazabar Jalingo/Yorro/Zing na majalisar jihar Taraba na gudana cikin kwanciyar hankali.
INEC na gudanar da zaben a kananan hukumomi ukun ne domin cike gurbin kujerar dan majalisar tarayyar su kamar yadda kotu ta bukata.
Duba sanarwar da INEC ta fitar a kasa:
An rantsar da Diri matsayin gwamnan Bayelsa karo na biyu
A wani labarin na yau Laraba, Legit Hausa ta ruwaito cewa Douye Diri, ya yi rantsuwar kama aiki matsayin gwamnan jihar Bayelsa a wa'adi na biyu.
Da misalin karfe 1:58 na rana, babban mai shari'a na jihar ya karanta wa Diri rantsuwar kama aikin a babban filin wasanni na Samson Siasia da ke babban birnin jihar, Yenagoa.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan na daga cikin wadanda suka halarci taron.
Asali: Legit.ng