Babban Labari: An Rantsar da Diri a Matsayin Gwamnan Bayelsa a Wa’adi Na Biyu

Babban Labari: An Rantsar da Diri a Matsayin Gwamnan Bayelsa a Wa’adi Na Biyu

  • Babban alkalin jihar Bayelsa, Mai shari'a Matilda Ayemieye ya rantsar da Douye Diri da Lawrence Ewhrudjakpo a matsayin gwamna da mataki
  • An rantsar da Diri matsayin gwamnan ne a wa'adi na biyu a babban filin wasanni na Samson Siasia da ke Yenagoa, birnin jihar
  • Manyan baki irin su Kashim Shettima, Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, da gwamnonin jihohi da dama sun halarci bikin rantsarwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Bayelsa - Rahotannin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa an rantsar da Duoye Diri a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Bayelsa.

Ya yi rantsuwar ne da misalin karfe 1:58 na ranar Laraba a filin wasanni na Samson Siasia da ke Yenagoa, babban birnin jihar, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shirin Pulaku: Gwamnati ta dauki mataki 1 tak na kawo karshen fadan makiyaya da manoma

An rantsar da Diri a matsayin gwamnan Bayelsa a wa’adi na biyu.
An rantsar da Diri a matsayin gwamnan Bayelsa a wa’adi na biyu. Hoto: @govdouyediri
Asali: Facebook

Diri da mataimakinsa Lawrence Ewhrudjakpo, sun yi rantsuwar kama aiki karkashin jagorancin babban alkalin jihar, Mai shari’a Matilda Ayemieye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan 'yan siyasar Najeriya sun halarci bikin rantsuwar

Manyan mutanen da suka halarci bikin rantsuwar sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, tsoffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Seyi Makinde (Oyo), Caleb Mutfwang (Plateau), Mohammed Bago (Niger).

Sauran sune, Ademola Adeleke (Osun), Godwin Obaseki (Edo), AbdulRahman AbdulRazak (Kwara) da kuma Ahmadu Fintiri (Adamawa).

Sauran sun hada da Sheriff Oborevwori (Delta), Siminalayi Fubara (Rivers), Umo Eno (Akwa Ibom), Hyacinth Alia (Benue) da Uba Sani (Kaduna).

Kusoshin jam'iyyar PDP sun hallara a wajen taron

Tsoffin shugabannin majalisar dattawa Bukola Saraki da Adolfus Wabara wanda yanzu shine shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP da kuma sauran shugabannin jam’iyyar na kasa da na jihohi suma sun halarci bikin.

Kara karanta wannan

BoT: Tsohon shugaban majalisar dattawa da tsohon gwamnan Kaduna sun samu manyan muƙamai

Dubban ‘yan jihar ne suka yi dafifi a filin wasam domin nuna godiya ga nasarar da gwamnan ya samu a zaben 11 ga Nuwamba, 2023, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Diri ya samu kuri'u 175,196 wanda hakan ya bashi nasara akan babban abokin hamayyarsa, Timipre Sylva na jam'iyyar All Progressives Congress.

Yan daba sun tarwatsa masu zabe a jihar Enugu - INEC

A hannu daya kuma, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa wasu 'yan daba sun tarwatsa masu zabe a mazabar Enugu ta Gabas da ke jihar Enugu.

Hukumar zabe ta kasa INEC ce ta sanar da hakan a ranar Laraba inda ta ce 'yan daban sun lalata gaba daya kayayyakin zaben.

Sai dai hukumar ta ce ba ta samu wani rahoton jikkata wani ba, kamar yadda ta wallafa bidiyon barnar da aka yi a wajen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.