Kotu Ta Sake Dakatar da EFCC Tuhumar Burgediya-Janar a Najeriya Kan Badakalar Kudade, Ta Fadi Dalili

Kotu Ta Sake Dakatar da EFCC Tuhumar Burgediya-Janar a Najeriya Kan Badakalar Kudade, Ta Fadi Dalili

  • Yayin da ake zargin babban soja kan badakalar kudade, Babbar Kotun Tarayya da dakatar da hukumar EFCC kan lamarin
  • Kotun ta dakatar da hukumar ce kan tuhumar Burgediya-Janar Charles Nengite kan zargin karkatar da kudade
  • Ana zargin Nengite da badakalar makudan kudade lokacin da ya ke kula da Hukumar NDDC ta Neja Delta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ci gaba da tuhumar wani babban soja.

Kotun ta dakatar da hukumar ce kan tuhumar Burgediya-Janar Charles Nengite kan zargin karkatar da kudade.

Kotu ta dakatar da EFCC kan tukumar babban soja
Kotu ta gargadi Hukumar EFCC kan tuhumar babban soja a Najeriya. Hoto: Federal High Court.
Asali: UGC

Wane hukunci kotun ta yanke a Abuja?

Kara karanta wannan

Kotun Musulunci ta aika Murja Kunya zuwa Kurkuku a Kano, An Bayyana Dalili

Ana zargin Nengite da badakalar makudan kudade lokacin da ya ke Hukumar NDDC ta Neja Delta, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Shari’a, Obiora Egwuatu shi ya yi hukuncin a ranar 29 ga watan Janairu wanda aka leko a yau Laraba 14 ga watan Faburairu a Abuja.

Obiora ya ce EFCC ba ta da ikon tuhumar sojan da ke kan aikinsa tun da kotun rundunar sojin ta dauki mataki a kansa.

Wane mataki kotun ta dauka kan EFCC?

Alkalin ya umarci hukumar ta dakatar da tuhumar da ta ke yi a cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 16 ga watan Yunin 2022.

Ya kuma ce duk wata tuhuma don hukunta shi kan zargin badakalar kudade ya haramta duba da kundin tsarin mulki.

Har ila yau, ya umarci hukumar ta biya tarar naira dubu 500 ga wanda ake zargi don matsalolin da suka saka shi, cewar Freedom Nigeria.

Kara karanta wannan

EFCC: An daure Mama Boko Haram a kurkuku na shekaru 10 saboda zambar N40m

Yan sanda sun cafke mai bai wa Bello Turji kaya

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar cafke wani tsohon sojan sama kan zargin alaka da ‘yan bindiga.

Wanda ake zargin Ahmed Mohammed an kore shi ne daga aikin bayan shafe shekaru biyar kan wani laifin da ya aikata.

Ana zargin sojan da safarar kayan sojoji ga kasurgumin dan bindiga Bello Turji daga Kaduna zuwa jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.