IMF Ta Fallasa Karyar Najeriya, Gwamnati Ta Dawo da Tallafin Man Fetur da Aka Cire
- Ana zargin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da cigaba da biyan tallafin man fetur har zuwa yanzu
- Shugaban kasar yana hawa mulki ya sanar da janye tsarin, hakan ya jawo farashi ya tashi nan take
- Hukumar IMF tana tunanin farashin da ake sayen mai yau ba shi ne hakikanin kudin lita a kasuwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Tun a ranar da aka rantsar da shi, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da duniya ya yi watsi da tsarin biyan tallafin man fetur.
Hukumar IMF mai bada lamuni na duniya, ya na zargin gwamnatin tarayya ta lashe amanta kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Zargin da IMF take yi shi ne gwamnatin Najeriya tana yi wa mutanenta rangwamen farashin fetur a kan hakikanin kudin lita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudin fetur ya ki canzawa
Bini-bini CBN ya kan sanar da canjin da aka samu wajen shigo da kaya daga ketare, amma farashin fetur bai motsa sosai ba.
A farkon makon nan, an saida Dalar Amurka a kan N1,499/$1 a bankuna, yayin da farashin kasuwar fage ya doshi N1500/$1.
IMF tana so fetur ya tashi
Jawabin da shugabannin IMF suka fitar a karshen makon jiya ya ce akwai yiwuwar gwamnati ta rike kudin fetur a gidajen mai.
Hukumar ta ba shugaba Bola Tinubu shawarar daina biyan duk wani nau’i na tallafin fetur domin samun kudin tafiyar da gwamnati.
Jaridar ta ce tun watan Satumba aka fahimci tsarin biyan tallafin fetur ya dawo a boye. An dade ana rade-radin dawo da tsarin.
Takardu sun tabbatar da kamfanin NLNG ya fitar da wasu kudi, ya biya $275m ta hannun NNPCL daga ciki ne aka cike gibin fetur.
Nawa ya kamata a saida fetur?
Tun da Naira ta karye zuwa N1, 499/$, ya kamata farashin litan fetur ya kai N1, 000.
Har yau mafi tsadan farashin da aka saida fetur bai zarce N720 ba. A gidajen man gwamnati na NNPCL, akwai inda lita ta ke N620.
A bi shawarar IMF ko a'a?
Mutane da-dama sun yi Allah-wadai da wannan shawara ta IMF, Femi Falana yana cikin masu ganin hakan ba zai taimaki kasar ba.
Rahotanni sun ce lauyan ya nemi gwamnati tayi watsi da kiraye-kirayen, kuma ta shiga sahun BRICS ta daina biyewa zancen IMF.
Asali: Legit.ng