Tsadar Rayuwa: Jam’iyyar PDP Ta Gaji da Adawa Marar Amfani, Za Ta Taimaki APC Kan Matsalar

Tsadar Rayuwa: Jam’iyyar PDP Ta Gaji da Adawa Marar Amfani, Za Ta Taimaki APC Kan Matsalar

  • Yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya, jam’iyyar PDP mai adawa a kasar ta yi martani tare da alkawarin samo mafita
  • Jam’iyyar ta ce madadin kushe tsare-tsaren gwamnati za ta yi kokarin yin adawa mai amfani ta hanyar neman mafita
  • Sanata Bala Mohammed, shugaban gwamnonin PDP shi ya bayyana haka yayin taron Kwamitin Amintattu a Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP, Sanata Bala Mohammed ya yi magana kan halin kunci da ake ciki a Najeriya.

Bala wanda shi ne gwamnan jihar Bauchi ya ce jam’iyyar za ta samar da hanyar bullewa kan matsalar ta hanyar adawa mai amfani, cewar Arise TV.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

Jami'yyar PDP za ta taimakawa APC kawo karshen matsalar tsadar rayuwa
Jam’iyyar PDP ta yanke shawarar taimakawa APC kan tsadar rayuwa. Hoto: Atiku Abubakar, Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Mene PDP ke cewa kan mulkin Tinubu?

Sanatan ya bayyana haka ne yayin ganawar Kwamitin Amintattun Jam’iyyar (BOT) a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan wanda ya koka kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki ya ce madadin kushe-kushe, jam’iyyar za ta samar da hanya mai inganci don dakile matsalar.

Ya yi alkawarin jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya kuma mafi karfin jam’iyya a Najeriya, cewar TheCable.

Ta koka kan halin da ake ciki

A cewarsa:

“Kwamitin amintattu ya damu kwarai kan halin da ake ciki na rashin tsaro da kasha-kashen jama’a babu kakkautawa.
“Wannan matsaloli duka sun samo asali ne ganin yadda tsare-tsaren jam’iyyar APC mai mulki suke a watanni tara da suka yi.
“Kwamitin ya kuma koka kan yadda cin hanci ya yi yawa musamman karkatar da kayan rage radadi na ‘yan Najeriya.”

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gama shiri, ta faɗi jiha 1 da zata ƙwace mulki daga hannun gwamnan PDP a 2024

Bala ya ce har ila yau, kwamitin ya kadu ganin yadda darajar naira ke kara dukushewa da kuma tsadar man fetur da kuma wahalar samun mai din.

APC ta nemi taimakon PDP kan halin kunci

A baya, kun ji rahoton cewa jam’iyyar APC mai mulki ta bukaci samar da wata hanyar kawo sauki daga jam’iyyar PDP.

Jam’iyyar ta ce madadin kushe-kushen da PDP ke yi ya kamata su samo wata hanya da za a samu saukin rayuwa.

Hakan ya biyo bayan mawuyacin hali da ‘yan kasar ke ciki tun bayan cire tallafi da kuma tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.