Hadimin Tinubu Ya Yi Bayanin Dalilin da Ya Sanya Najeriya Ta Kasance Matalauciyar Kasa
- Wani hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya ce Najeriya ƙasa ce matalauciya kuma yadda mutane ke kallon arziƙinta bai kai nan ba
- Onanuga ya ce mafi ƙarancin albashin Najeriya na N33,000 ($39) idan aka kwatanta da na Afrika ta Kudu $240, hakan ya nuna ƙarara cewa Najeriya ƙasa ce mai fama da talauci
- Ya ce yana fatan matsin da aka yi wa tattalin arziƙin ƙasar nan zai ragu saboda cire tallafin man fetur da kuma mayar farashin sauya kuɗi ya zama ɗaya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, ya ce Najeriya ƙasa ce matalauciya kuma mutane ba su san haƙiƙanin ƙiyasin arziƙinta ba.
Onanuga ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise tv a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairun 2024.
Ya ce har yanzu Najeriya ƙasa ce mai matuƙar talauci idan aka kwatanta da sauran ƙasashen Afirika wajen samun ƙarancin kuɗaɗen shiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Onanuga ya ce kan arziƙin Najeriya?
Mai taimakawa shugaban ƙasar ya ce:
"Ƙasarmu ƙasa ce mai matuƙar talauci. Ina tunanin ba su san haƙiƙan ƙiyasin tattalin arziƙin ƙasarmu ba. Ina ganin mun wuce gona da iri wajen ƙiyasin arziƙinmu.
"Dangane da mafi ƙarancin albashi, mafi ƙarancin albashin Afirka ta Kudu kusan $240 ne a kowane wata. A Najeriya, N33,000 shi ne kusan $39 a wata. Dubi tazarar, kun ga hakan ma yana nunawa a cikin wasu ɓangaren albashin.
"Ƙididdigar talauci tana nan. A bayyane yake muna da ita, sannan mutane suna cikin talauci wanda hakan shi ya sanya a lokacin da muka samu wannan matsalar da muke fuskanta, ba za su iya daidaitawa ba saboda ba mu da rarar kuɗaden shiga. Lamari ne mai matuƙar takaici kuma gwamnati ta damu matuƙa.
Onanuga ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu "tana fatan matsin lambar da muke fuskanta zai ragu" tare da cire tallafin man fetur da kuma haɗa kan farashin canji.
Sarkin Kano Ya Aike da Saƙo Ga Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya aike da saƙo ga Shugaba Tinubu kan halin matsin da ake ciki a ƙasa.
Srkin na Kano ya ba da saƙonne ga uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu, bayan ta ziyarci fadarsa da ke birnin Kano.
Asali: Legit.ng