‘Yan Sanda Sun Kama 'Yan Fashin da Suka Farmaki Kwamishina a Jihar Arewa

‘Yan Sanda Sun Kama 'Yan Fashin da Suka Farmaki Kwamishina a Jihar Arewa

  • Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutum hudu da ake zargi da yi wa kwamishinan jihar Adamawa fashi
  • A daren ranar Lahadi ne 'yan fashin suka farmaki gidan Muhammed Sadiq Wali tare da sace motarsa da wasu muhimman abubuwa
  • Sai dai kuma, rundunar 'yan sandan ta tabbatar da kwato motar kwamishinan da wasu makamai daga wajen wadanda ake zargin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Adamawa - Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutum hudu, wadanda ake zargi da yi wa kwamishinan jihar mai ci fashi.

Wadanda ake zargin sun farmaki kwamishinan, Muhammed Sadiq Wali a motarsa ta aiki sannan suka yi masa fashin wasu muhimman abubuwa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan daba suka farmaki kwamishina a jihar Arewa, sun sace motarsa

'Yan sanda sun kama wadanda suka farmaki kwamishina
‘Yan Sanda Sun Kama 'Yan Fashin da Suka Farmaki Kwamishina a Jihar Arewa Hoto: Mohammed Sadiq
Asali: Facebook

Jami'an tsaron sun kuma yi nasarar kwato motar Totota Hilux da 'yan fashin suka sace, karamar bindiga, harsasai uku, wayoyin hannu, kudaden waje da sauransu, Nigerian Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan fashin da aka kama sun hada da Salihu Buhari mai shekaru 38, Abdullahi Abubakar mai shekaru 35, mazaunin Garoua a kasar Kamaru.

Sauran sune Isa Adamu mai shekaru 55 daga Tudun Wada, jihar Sokoto da kuma Mustapha Muhammed, mai shekaru 47 daga Lelewalji, karamar hukumar Girei ta jihar Adamawa.

Me rundunar 'yan sandan ta ce?

Wata sanarwa daga kakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu, rahoton Leadership.

SP Nguroje ya ce:

“Tawagar jami’an ‘yan sanda na hadin gwiwa da ke hedikwatar ‘yan sanda ta Girei ta kama wadanda suka aikata laifin bayan sun kai hari gidan kwamishinan da abin ya shafa tare da yi masa fashin mota da sauransu.

Kara karanta wannan

An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci

"Nasarar ta biyo bayan wani dabarun gudanar da aiki da rundunar ta bullo da shi na duba laifukan da suka hada da fashi da makami.
"Ta’addancin 'yan shilla, da garkuwa da mutane a ciki da wajen babban birnin jihar, kuma ta ba da tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin.”

Yan daba sun sace motar kwamishinan Adamawa

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai farmaki kan kwamishinan Muhalli a jihar Adamawa.

Maharan sun farmaki Mohammed Sadiq ne a daren jiya Lahadi 11 ga watan Faburairu tare da sace motar da yake hawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng