Bamu da Shirin Kara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya In Ji NNPCL

Bamu da Shirin Kara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya In Ji NNPCL

  • Kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya musanta rahoton cewa farashin fetur na zai ƙara tashi a faɗin Najeriya
  • A wata sanarwa da mahukuntan NNPCL suka fitar ranar Jumu'a, sun ce kamfanin ba shi niyyar ƙara tsadar mai
  • Tun bayan cire tallafin mai, NNPCL ya ƙara farashin lita aƙalla sau biyu, lamarin da ya jefa 'yan Najeriya cikin matsin rayuwa

FCT Abuja - Kamfanin mai na gwamnatin Najeriya (NNPCL) ya ce ba bu wani shiri na ƙara tashin farashin litar man fetur daga farashin N620 kan kowace lita.

Kamfanin ya musanta rahoton da ke yawo a soshiyal midiya wanda ya yi iƙirarin cewa farashin Premium Motor Spirit (PMS) wanda aka fi sani da Fetur na dab ta ƙara tsada a ƙasar nan.

Kamfanin NNPCL ya musanta ƙara farashin fetur.
Bamu da Shirin Kara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya In Ji NNPCL Hoto: NNPC Limited
Asali: UGC

Da gaake ana shirin ƙara tsadar man fetur?

Kara karanta wannan

Babbar Matsala 1 Da Aka Gano Bayan Taron da Atiku Ya Gudanar Kan Shugaba Tinubu a Abuja

Sai dai NNPCL ya musanta batun a wata sanarwa da ya wallafa a shafin kamfanin na manhajar X ranar Jumu'a, 6 ga watan Oktoba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPC wanda ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya ya ce ba shi da niyyar ƙara farashin fetur kamar yadda ake ta yaɗa wa a soshiyal midiya.

A cewar kamfanin mai na NNPC Limited, gidajen sayar da mai da ke ƙarƙashinsa suna sayar da mai da sauran kayayyaki masu inganci kuma a farashi mai sauki.

A sanarwan da ya fitar, NNPCL ya ce:

"Ya ku masu girma abokan ciniki, mu a kamfanin NNPC muna jin daɗin hulɗa da ku, kuma ba mu da niyyar ƙara farashin litar PMS watau man fetur kamar yadda ake hasashe."
"Da fatan za a sayi kayan mu masu inganci akan farashi mafi arha a gidajen sayar da mai na NNPC a fadin kasar nan."

Kara karanta wannan

Kuma Ku Dana: Gwamnan APC Mai Shirin Barin Mulki Ya Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci

Tun bayan lokacin da gwamnatin tarayya ta ayyana cewa ta tuge tallafin man fetur, aƙalla sau biyu NNPCL ya sanar da ƙarin farashin fetur a faɗin Najeriya.

Cire tallafin ya haddasa karuwar wahalhalu da tsadar kayan abinci wanda ya taɓa akasarin 'yan Najeriya, da yawa suka wayi gari cikin ƙuncin rayuwa.

Kotun Zaɓe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan LP a Zaben 2023

A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta sha kashi a ƙarar da ta shigar tare da ɗan takararta suna masu kalubalantar nasarar gwamna Otti na jihar Abiya.

Yayin yanke hukunci ranar Jumu'a, Kotun zaɓe mai zama a Umuahia ta kori karar bisa rashin cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel