Ma’aikacin CBN Ya Fadawa Kotu Yadda Emefiele Ya Cire $6.23m Lokacin Zaben 2023
- An cigaba da shari’ar da ake yi tsakanin hukumar EFCC da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Wannan karo Ogau Onyeka Michael ya bada shaida a kan yadda aka umarce shi ya biya wasu $6.2m
- An fitar da kudin ne da sunan jami’an kasashen waje da ke aikin kula da sa ido a zaben Najeriya a 2023
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ogau Onyeka Michael babban ma’aikaci ne a bankin CBN, an kira shi ya bada shaida a shari’ar Godwin Emefiele da EFCC.
Daily Trust ta rahoto cewa Ogau Onyeka Michael ya yi bayanin abin da ya sa aka biya masu lura da zabe kudi $6,230,000 a 2023.
EFCC ta kira shaida a kan Emefiele
Ma’aikacin babban bankin shi ne shaidan farko da gwamnati ta kira a shari’ar da ake yi gaban Hamza Muazu a babban kotun tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin Godwin Emefiele da karya da yaudara wajen samun damar karbar $6,230,000 da sunan biyan masu aikin sa idon zabe.
Da aka dawo kotu a ranar Litinin, Rotimi Oyedepo (SAN) ya kira Ogau Onyeka Michael domin ya kafa hujja da shi a gaban alkali.
An umarci a cire $6.23m daga CBN
Shaidan ya ce a ranar 8 ga watan Junairun 2023, aka kawo takardu ofishinsa domin ya biya $6,230,000 ga masu sa ido a zaben shekarar.
Akwai wakilai da aka saba turowa daga kasashen waje domin lura da zabukan Najeriya, an yi irin haka a zaben 2023 da aka shirya.
EFCC ta rahoto jami’in bankin yana cewa hadiminsa ya nuna masa takardar da aka aiko dauke da sa hannun Darektan harkokin banki.
Abin da takardar ta kunsa shi ne a biya tsabar kudi har $6,230,000 ga wani ma’aikaci da ke ofishin SGF da nufin a sa ido a babban zabe.
An bar Godwin Emefiele a matsala
Premium Times ta ce an yi alkawari za a biya wadanan kudi a tsakiyar shekarar 2023, ma’aikatar tattalin arziki aka bari da dawainiyar.
Duk da Muhammadu Buhari ya yi na’am da wannan bukata, amma ba a biya kudin ba sai a watan Afrilu, watanni bayan an gama zaben.
An kashe biliyoyi a ma'aikatu 256
Ana da labarin cewa an gano abin da wasu hukumomin 256 suka kashe ya kai N361bn alhali N76bn aka sa hannu za su batar a 2020.
Sashe na 80 (2) na kundin tsarin mulkin 1999 ya hana a taba kudi daga asusu ba tare da ka’ida ba, wannan ya nuna an sabawa dokokin aiki.
Asali: Legit.ng