Ma’aikatu da Hukumomi 256 Sun Yi Kaca-kaca da N256bn ba da Sanin Gwamnati ba

Ma’aikatu da Hukumomi 256 Sun Yi Kaca-kaca da N256bn ba da Sanin Gwamnati ba

  • Babban mai binciken kudi ya gabatar da rahoton yadda ma’aikatu su ka rika bindiga da kudi
  • Hukumomi, cibiyoyi da ma’aikatun gwamnati sun batar da dukiyoyin da ba ayi kasafi da su ba
  • A dokar kasa, kashe kudin da bai cikin kudin kasafin shekara ya sabawa tsarin mulkin Najeriya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ofishin babban mai binciken kudi a gwamnatin tarayya ya zargi hukumomi, ma’aikatu da cibiyoyi kusan 256 da sabawa doka.

Punch ta ce wadannan ma’aikatun gwamnati sun saba ka’ida ne ta hanyar kashe biliyoyin kudin da ba ayi kasafi da su a 2020 ba.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari a lokacin yana mulki Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Wadanda abin ya shafa kamar yadda aka gano daga rahoton da OAuGF ya mikawa majalisa sun hada da cibiyar fasaha ta sojin sama.

Kara karanta wannan

NLC: Ma’aikata Za Su Bukaci N1m a Matsayin Mafi Karancin Albashi a Kowane Wata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da doka ta ce a kan kudin gwamnati

Ya kamata mai binciken kudin gwamnatin ya gabatar da wannan rahoto ne tun 2021, sai dai ba a iya yin hakan ba sai Nuwamban 2023.

Sashe na 80 (2) na kundin tsarin mulkin 1999 ya haramta a cire kudi daga asusun tarayya na CRF ba tare da ya shiga kundin kasafi ba.

Wannan doka ta hana ma’aikatun tarayya su batar da N361bn maimakon N76bn da aka ware masu a kasafin kudin shekarar 2020.

Rahoton ya zargi akantocin wadannan ma’aikatu da kin bin tsarin kasafi da watsi da ka’idoji.

Wasu ma’aikatu da cibiyoyin gwamnatin kasar suna kashe bangaren kudin da suka tatso domin dawainiya da kansu da ma’aikatansu.

Misalan facaka da kudin gwamnati

Binciken AuGF ya bayyana yadda aka yi kasafin N7bn domin biyan hakkokin ma’aikata, amma ma’aikatun nan suka kashe N335bn.

Kara karanta wannan

Wani jigo a APC ya gargadi Gwamnati, bai so ayi wa ma’aikata karin albashi sosai

Akwai ma’aikatu fiye da 100 da suka kashe kudi da ya zarce wanda aka ware masu a shekarar, New Telegraph ta tabbatar da labarin nan.

N14bn sun tafi wajen biyan tallafi ba tare da majalisar tarayya ta amince da kasafinsa ba.

Gwamnati ta zargi DisCos da yaudara

Rahoton nan ya nuna gwamnatin tarayya ta na sa ido a kan yadda kamfanonin ‘yan kasuwa su ke cin kudin lantarki daga hannun jama'a.

Kamfanonin da ake kira DisCos sun yaudari mutane miliyan 7 a lissafin biyan kudin wuta daga Junairu zuwa Satumban shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng