Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020

Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya saka hannu a kan kasafin kudin shekarar 2020 da aka yi wa kwaskwarima.

A cewar Tolu Ogunlesi, mataimakin shugaban kasar na musamman a kan sabbin kafafen watsa labarai, shugaban kasar ya sanya hannu a kan gyararren kasafin kudin misalin karfe 11.04 na safiyar ranar Juma'a.

Najeriya ta yi wa kasafin kudin ta kwaskwarima ne bayan faduwar farashin danyen man fetur a kasuwanin duniya da kuma bullar annobar COVID-19 da ya janyo tsaiko a kan hada hadar kasuwanci a duniya.

Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020
Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020. Hoto daga fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020
Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020. Hoto daga fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Modo Sheriff ya kai ziyarar bazata sakatariyar APC da ke Abuja

Buhari ya ce, "Hasashen da aka yi game da Dokar Daidaito ta 2020 ba za su yi wu ba."

Ministan Kudi da Kasafin Kudi, Zainab Ahmed ta shaidawa yan majalisa a ranar Alhamis cewa shugaban kasar zai rattaba hannu a kan kasafin kudin da aka yi wa kwaskwarima a ranar Juma'a.

Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020
Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020. Hoto fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020
Buhari ya sanya hannu kan gyararren kasafin kudin 2020. Hoto daga fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

A baya, Legit.ng ta kawo muku cewa kwanaki 29 da suka gabata, Majalisar wakilan kasar nan ta amince da gyararren kasafin kudin 2020 inda ta kara shi daga Naira tiriliyan 10.5 zuwa Naira tiriliyan 10.8.

Duk da cewa kwamitin kula da kasafin kudin wanda rahotonsu aka yi amfani da shi a majalisar a ranar Laraba, sun bukaci a yi amfani da N10,801,544,664,642.

'Yan majalisar sun kara da Naira biliyan hudu na walwalar kungiyar likitoci masu neman kwarewa bayan barazanar yajin aiki da suka yi.

Hakazalika, majalisar ta amincewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbo aron zunzurutun kudi har Dala biliyan 5.513 don amfanin kasar nan.

Bugu da kari, Gwamnatin tarayya ta sanya takunkunmi kan daukan aikin yi a ma'aikatun gwamnatin tarayya gaba daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel