Yanzu nan: Rahoton karshe na kasafin kudin 2020 ya shiga Majalisar Dattawa

Yanzu nan: Rahoton karshe na kasafin kudin 2020 ya shiga Majalisar Dattawa

A yau Ranar Laraba, aikin karshen da aka yi a kan kundin kasafin kudin shekarar 2020 ya dawo cikin zauren majalisar dattawan Najeriya. Sanata Barau Jibrin ne ya gabatar da rahoton kasafin.

Kwamitin kasafin kudi wanda Barau Jibrin mai wakiltar Arewacin jihar Kano ya ke jagoranta a majalisar dattawa ya karkare aikinsa. Ya kamata ace an karasa wannan aiki tun a makon jiya.

Wannan kwamiti mai kula da aikin kasafin kasar ya nemi alfarmar karin ‘yan kwanaki daga Ranar 26 da aka bada a matsayin wa’adin karkare aikin na shekarar badi zuwa jiya Ranar Talata.

Sai dai a jiya Majalisa ba ta iya zama ba domin makokin wani ‘Dan majalisa mai wakiltar Magama da Rijau da ya rasu. A yau Laraba, 4 ga Watan Disamban 2019 ne Majalisar ta dawo aiki.

KU KARANTA: Buhari ya kama hanyar kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa abin da ya rage yanzu shi ne Sanatocin kasar su duba shawarwarin da kwamitin ya bada. Za a yi wannan ne a cikin ragowar kwanakin makon nan.

A na sa ran cewa daga an duba rahoton da ‘ya ‘yan kwamitin su ka shirya, majalisar kasar za ta hadu ta amince da kasafin. Daga nan kuma sai a mika kundin gaban shugaban kasa ya sa hannu.

Bata lokacin da aka rika yi wajen kare kasafin kudin a gaban majalisa ya na cikin abin da ya jawo aka kai yanzu kundin kasafin kudin bai bar hannun ‘yan majalisa zuwa fadar shugaban kasa ba.

Bisa dukkan alamu, nan da ‘yan kwanaki za a aikawa shugaba Muhammadu Buhari kasafin na sa na Naira tiriliyan 10.33, wanda ake sa rai zai shiga doka, har a soma amfani da shi a farkon 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel