Tashin Hankali Yayin da Ƴan Bindiga Suka Halaka Ƴan Kasuwa Kusan 10 a Jihar Arewa
- Yan bindiga sun halaka ƴan kasuwa 9 a kan hanyar komawa gida bayan tashi daga kasuwar Jibia ranar Lahadi da yamma
- Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kuma ƙona motoci biyu da ƴan kasuwar ke ciki kuma ana zargin sun yi garkuwa da wasu
- Wannan lamari na zuwa ne yayin Malam Dikko Radda ya ce an fara samun zaman lafiya a jihar sakamakon kokarin jami'an tsaro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Wasu mahara da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun halaka ƴan kasuwa 9 a titin Jibia zuwa Batsari da ke jihar Katsina ranar Lahadi da yamma.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan kasuwan na kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar Jibia lokacin da suka faɗa tarkon ƴan bindiga da misalin ƙarfe 6:00 na yammaci.
Jaridar Punch ta tattaro cewa ƴan kasuwar da lamarin ya shafa sun taho ne a cikin motoci biyu, waɗanda ƴan bindigan suka ƙona bayan kashe su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
"Ƴan kasuwar sun tashi da wuri-wuri bayan sun gama cin kasuwa ranar Lahadi, kuma ɓa zato suka ci karo da ƴan bindiga a tsakanin karfe 5-6 na yamma a titin Jibia-Batsari."
A cewarsa, ƴan bindigan sun buɗe wa motoci biyu da ƴan kasuwar ke ciki wuta, suka halaka diraba ɗaya da dukkan ƴan kasuwan da ke ciki. Sun koma ƙona motocin.
Bayan faruwar lamarin, mutane suka ɗauke gawarwakin suka kai su babban asibitin Jibia, inda ƴan uwansu suka je suka ɗauka washe hari ranar Litinin (yau).
Ƴan bindiga sun sace wasu yan kasuwa ne a harin?
Babu cikakken bayani kan adadin ƴan kasuwar da suka ji raunuka sanadin harin da kuma yawan waɗanda mai yiwuwa ƴan bindigan suka sace har zuwa safiyar yau Litinin.
Haka nan kuma kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasiru Mu'azu, bai ce komai ba dangane da wannan sabon harin.
Da aka tuntubi kakakin ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu, ya ce yana cikin taro kuma bai turo amsar saƙonnin tes da aka tura masa ba.
Yan bindiga sun halaka lauya a Imo?
A wani rahoton kuma Wasu ƴan bindiga da ba a sani ba sun halaka Barista Victor Onwubiko, a kan hanyarsa ta komawa jami'ar jihar Abia daga mahaifarsa a Imo
Rahotanni sun bayyana cewa lauyan ya rasa ransa ne ranar Asabar da daddare a kan titin Okigwe zuwa Oturu, wanda ake yawan kai hare-hare.
Asali: Legit.ng