Kaduna: Shugaban Karamar Hukuma Ya Ba Wa DPO Kyautar Naira Miliyan 1 Akan Wani Dalili 1 Tak
- Shugaban ofishin rundunar 'yan sandan Tafa, karamar hukumar Kagarko, jihar Kaduna, DPO Idris Ibrahim ya samu kyautar naira miliyan 1.
- Shugaban karamar hukumar Kagarko ne ya ba jami'in dan sandan kyautar wannan kudi saboda yaki karbar cin hanci daga hannun wani ɗan bindiga
- Rahotanni sun bayyana cewa mai garkuwa da mutane ya ba Ibrahim cin hancin makudan kudade don ya kyale shi ya gudu bayan da aka kama shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna - Shugaban karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, Hon. Nasara Rabo, ya ba wa wani jami’in ‘yan sanda (DPO) mai suna Idris Ibrahim kyautar naira miliyan 1.
Hon Rabo ya ba wa DPO tukuicin kudin ne saboda ya ki amincewa da karbar makudan kudade da wani mai garkuwa da mutane ne ya bayar domin a datse bincikensa.
Ibrahim na aiki a matsayin DPO na ofishin 'yan sandan Tafa, karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Guardian ta ruwaito cewa DPO Ibrahim ya kama mai garkuwa da mutanen ne a ranar 22 ga watan Janairun 2024.
Takardar jinjina da kyautar naira miliyan 1
Sai dai mai garkuwa da mutanen ya yi yunkurin ba wa Ibrahim cin hancin makudan kudade domin a datse binciken amma dan sandan ya ki karbar tayin kudin.
"Wannan yunƙuri guda ɗaya da ka yi ba wai kawai ya sa rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi alfahari ba, har ma ya sanya mutanen Kagarko, Kaduna da Nijeriya gaba ɗaya jinjina maka.
“Da wannan ne kuma majalisata da ma’aikatan karamar hukumar Kagarko suna mika maka takardar yabo tare da ba ka kyautar naira miliyan daya a matsayin kwarin gwiwa don kara himma da kishin kasa."
- A cewar Hon. Nasara Rabo
Nasara ya bukaci daukacin jami’an ‘yan sanda a jihar da su rika kiyaye da’ar aikin su ta hanyar kin amincewa a hada baki da su wajen kawo cikas ga tsaron kasa.
Mai garkuwa da mutane ya ba dan sanda cin hanci N8.5m
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani dan bindiga da ake zargin mai garkuwa da mutane ne ya ba wani jami'in dan sanda cin hanci naira miliyan 8.5.
Lamarin ya faru ne a garin Jalingo, jihar Taraba, bayan da aka kama dan bindigar yayin da ya karbo kudin fansar wani da suka yi garkuwa da shi.
Sai dai kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Eribo ya ce jami'in na su yaki karbar kudin, kuma ya kama wanda ake zargin don yi masa tuhuma.
Asali: Legit.ng