Mummunar Gobara Ta Tashi a Ofishin ’Yan Sandan Kano
- Da sanyin safiyar yau Litinin ne wata mummunar gobara ta tashi a ofishin rundunar 'yan sandan Kano da ke Nasarawa
- Rahotanni sun bayyana cewa wani bangare na ofishin 'yan sandan ya kone kurmus yayin da aka killace takardu da makamai
- Kwamishinan'yan sandan jihar, Mista Usaini Gumel ya sanar da hakan yana mai cewa an fara tantance takardun da abin ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce gobara ta kone ofishin ‘yan sanda reshen karamar hukumar Nasarawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Usaini Gumel, ya bayyana hakan a Kano, inda ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin.
Daily Nigerian ta ruwaito kwamishinan yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Da misalin karfe 05.45 na safe, hedikwatar ‘yan sanda ta kama wuta kuma wani bangare na ginin ya kone gaba daya.
"Wannan ya faru duk da kokarin da hukumar kashe gobara ta Jihar ta yi na shawo kan wutar."
An fara tantance takardun da gobarar ta lalata
Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
“Tuni aka killace yankin domin hana mutane shiga, hakazalika makamai da alburusai da ke ofishin suna nan inda suke.
"A halin yanzu babban jami'in 'yan sanda na ofishin yana tantance wasu takardun da abin ya shafa."
- A cewar Usaini Gumel
Hedikwatar 'yan ‘yan sandan Kano ta kone kurmus
Tun a farkon shekarar ne Legit Hausa ta ruwaito maku vewa hedkwatar rundunar ‘yan sandan Kano da ke Bompai ta kone kurmus a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu.
An tattaro cewa gobarar da ta tashi a ofishin provost, ta bazu zuwa sashen kudi, dakin taro, ofishin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, ofishin mataimakan kwamishinan ‘yan sanda.
An kuma ruwaito cewa daukacin ofisoshin da ke saman bene na rundunar ‘yan sandan da aka gina a shekarar 1967 ne gobarar ta kone su, yayin da wutar ba ta shafi ofishin kwamishinan ‘yan sandan ba.
Asali: Legit.ng