An Tafka Asarar Dukiyar Miliyoyin Naira Yayin Da Tankar Man Fetur Ta Kama Da Wuta A Gidan Mai

An Tafka Asarar Dukiyar Miliyoyin Naira Yayin Da Tankar Man Fetur Ta Kama Da Wuta A Gidan Mai

  • Wata tankar dakon man fetur ta yi gobara a garin Idanre da ke karamar hukumar Idanre na jihar Ondo a daren ranar Asabar 18 ga watan Fabrairu
  • Wani ganau ya ce tankar man fetur din ta shigo gidan mai ta yi fakin ana sauke mai cikin tankin karkashin kasa ne kwatsam ta kuma da wuta kuma kowa ya tsere
  • Rahotanni sun nuna cewa gobarar ya yi sanadin kone dukkan kayayyakin da ke gidan man fetur din da abin da ke cikin wani gida da ke makwabtaka da gidan man

Jihar Ondo - An tafka asarar dukiyar miliyoyin naira yayin da wata tanka dauke da man fetur da fadi ta kama da wuta a garin Idanre da ke karamar hukumar Idanre a ranar Asabar da yama.

An tattaro cewa wutan ya kona gidan mai da wani gida da ke kusa da shi. Amma dai ba a rasa rai ba amma kayan da ke gidan man da ginin da ke kusa da shi duk sun kone.

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

Gidan Mai
Jami'an kashe gobara na kokarin kashe wuta a gidan mai a Legas. Hoto: NAN
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ganau ya ce tankar wacce ke dauke da man fetur da aka fi sani da PMS ya taho gidan man ne domin sauke fetur ta wani babban bututu lokacin da ya kama da wuta.

Shaidan gani da idon ya ce:

"Tankan ya iso gidan man yau da yamma kuma ma'aikata sun fara sauke man zuwa wani tanki na karkashin kasa, kwatsam dai wuta ta tashi kuma kowa ya tsere.
"Ta kona gidan man baki daya da gidan da ke kusa da gidan man shima ya kone. Amma daga bisani masu kashe gobara sun taho sun kashe wutan."

Martanin yan sandan jihar Osun

A yayin da aka tuntube ta, mai magana da yawun yan sandan jihar Mrs Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kara da cewa ba a rasa rai ba sakamakon gobarar.

Kara karanta wannan

Abincin N220k: Gidan cin abincin Gusto ya fadi gaskiyar labarin 'yan mata da Abdul a Gusto

Kakakin yan sandan ta ce:

"Zuwa cikin gaggawa da jami'an hukumar kashe gobara suka yi ya hana gobarar bazuwa tare da kara barna."

An yi asarar dukiya sakamakon gobara a hedikwatar rundunar yan sandan Najeriya ta Kano

A wani rahoton, kun ji cewa an rasa kayayyaki na miliyoyi yayin gobara da ta tashi a hedkwatar rundunar yan sandan Najeriya da ke Bompai, karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.

Wani ganau ya fada wa Daily Sun cewa wutar ta fara ci ne misalin karfe 2 na ranar Asabar kuma ya ce ta lakume wasu ofisoshi ciki har da na Provost da mataimakin kwamishina na yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel